Hanyoyin magance hatsarin tankuna mai a hanyoyinmu

Spread the love

Daga HASSAN IMRAN 

A makon da ya gabata, aka samu wani hatsarin tankar man fetur da ta kife a kan hanyar Dikko da ke Ƙaramar Hukumar Gurara a Jihar Neja. Tashar Talabijin ta Channel ta rawaito cewa an yi asarar rayuka saba’in da bakwai. Haka zalika, wasu da suka raunata an garzaya da su zuwa asibitin gwamnati da ke Suleja a inda ake jinyarsu. Harwayau, an sake wata gobarar tankar mai a ranar Asabar da ta wuce a garin Inugu a yayin da aka rawaito cewa an yi asarar rayuka sha takwas kuma an samu damar kuɓutar da mutane goma sha uku da gobarar ta rutsa da su. Motoci goma sha daya suka ƙone ƙurmus.

Wannan masifar da ibtila’i da ta auku, ta yi matuƙar tayar wa da ‘yan Nijeriya hankali, inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa akan yadda za a magance wannan matsala ta faɗuwar tankokin mai, wanda ke musababin gobarar. A gaskiya akwai ganganci da son banza da da yawan matasa ke fama da shi, a wannan hatsarin faɗuwar tankunan mai da yawa matasa su kan farmaki inda tanka ta faɗi domin ɗibar mai da cikin ganganci da garaje, kamar masu ɗibar ganimar yaƙi. Masu iya magana na cewa, ƙuda wajen kwaɗayi yakan mutu, kuma a garin gyaran gira ake rasa ido. Da yawa wannan gobarar tana rutsawa da su ne a yayin ɗibar man. Wannan babban kuskure ne da yakamata al’umma su kiyaye. Haka zalika, a yayin faɗuwar takunan man, akan samu wasu matasa  suna zuwa wuraren tankunan man domin yin bidiyo kan abinda yake faruwa, domin su wallafa shi a shafukan su na zaurukan sada zumunta. Wannan ma babu hikima a ciki, domin wannan ganganci ne kuma jefa kai zuwa halaka ne. Musulunci ya hane mu da jefa kawunanmu cikin duk abinda zai jefa rayuwarmu cikin hatsari.

Daga cikin dalilai da ke janyo wannan faɗuwar tankuna mai Shi ne rashin kyan hanyoyinmu. Da yawa daga cikin hanyoyin ƙasar nan a lalace suke; ga ramumuka kamar na burgu da sauran su. Harwayau, wasu dirbobin basu kula da lafiyar motocinsu kafin su hau hanya da ita. Rashin kiyaye dokokin tuƙi da kuma tuƙin ganganci Shi ma na cikin musabbabin gobarar tankunan mai. Shan barasa da sauran kayan sa maye kafin tuƙi na daga cikin abubuwan da ke janyowa matsalolin tuƙi a hanya.

Kamfuna masu bada motocinsu ga direbobinsu ya kamata suna kulawa da motocinsu. Idan mota na buƙatar a canza mata tayoyi, yakamata a canza ɗin, in kuma birkin mota ne ke da matsala  a gyara shi akan lokaci, domin kiyaye faruwar wani hatsari. Gwamnati na da nata kaso wajen gyaran hanyoyin da kuma ƙarfafa hukumar da ke kula da tsaron hanyoyi wajen ganin ana kiyaye ƙa’idojin tuƙi yadda yakamata. Yana da muhimmanci Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta fara yi wa dirbobi gwaji domin tatance masu lafiyar ƙwaƙwalwa daga wanda suke ta’amuli dumu-dumu da miyagun ƙwayoyi. Masu shan kayan barasa yakamata a hanasu tuki domin rage hatsarin motoci a hanya.

Allah Ya taƙaita mana masifu, Ya kuma shige mana gaba a harkokin mu. Allah Ya jiƙan waɗanda hatsarin tankunan mai ya rutsa da su ya kuma bada lafiya ga masu jinya. Amin
Hassan Imran ya aiko da wannan nasiha ne daga Jos, kuma za a iya samun sa kan addreshinsa na yanar gizo kamar haka; [email protected]

By ukarofi