Daga ALI ABUBAKAR SADIK
Wato babbbar annobar da ta faɗa wa Arewa, wadda ta rusa ta kuma ta ke ci gaba da rusa ta ita ce, watsi da tarbiyar Musulunci mafi mahimmanci da ta gindaya adalci da Allah ya wajabta mana a cikin suratul Nisa’I; Q4:135: “Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayuwa da ãdalci, mãsu shaida sabõda Allah, kuma kõ dã a kanku ne kõ kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida kõ a kansa) ya kasance mawadãci kõ matalauci, to, Allah ne mafi cancanta da al’amarinsu. Sabõda haka, kada ku bĩbiyi son zũciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, kõ kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Yã kasance Masani ga abin da kuke aikatãwa.”
Ayar da Annabi (SAW) ya ba mu cikakken tafsirinta a hadisin da Bukhari da Muslim suka ruwaito inda wata ’yar babban gida ta ƙabilar Makhzoum ta yi sata, amma saboda hali irin na ‘elitism’, sai wasu sahabbai su ka sako Usama Bn Zaid a gaba (wato aboki ga Manzo) da a nema mata afuwa. Nan take cikin fushi sai Annabi (SAW) ya miƙe ya ce, “Al’ummoni gabaninku sun halaka sakamakon duk sanda wani babba ya yi sata sai a kau da kai (elitism), amma idan talaka ne sai a yi masa hukunci. To, wallahi idan Faɗima za ta yi sata sai na tsayar mata da hukuncin Allah.”
Babu wata fassara ta waccan ayar ta Nisa’i irin wannan hadisi, wanda ke nuna cewa, adalci ba ruwansa da dangantaka ko wacce iri.
Amma a yanzu mu na kare gaskiya da yin adalci ne kaɗai, idan ya shafe mu ko iyalinmu ko ƙabilarmu, jinsinmu, siyasarmu, aƙidarmu ko addininmu. Saɓanin haka ba wanda zai kare gaskiya ko kiran adalci saɓanin wannan jerin illa ƙalilan. Kuma a bayyane ya ke cewa, babu wata ƙungiya a yau da take yaƙi da tsayar da irin wannan adalci irin ƙungiyar Izala, domin duk wanda ya saɓa wa wata fahimta tasu za a yi masa ca! ba tare da duba da uzurin cewa, akwai ƙamshin gaskiya ko babu ba. Domin mu na gani hatta Sheikh Ahmad Gumi, wanda mahaifinsa ne ya assasa Izala a ƙasar nan, bai tsira daga farmakinsu ba, saboda kawai ya saɓa wata fahimta tasu.
Wanna tabi’a ta rashin yin adalci, ba kawai ’yan Izala ba ne, a’a, kusan dukkanmu ne, kuma ita ke ruguza duk wata ni’imar da aka san Arewa da ita, abinda ya haifar mana da halin ha’ula’in da muka sami kanmu a ciki.
Haƙiƙa Ɗan Bello ya kawo zarge-zarge kan Sheikh Bala Lau da ƙungiyar Izala. Wataƙila idan da za a tsaya a yi adalci wajen nazarin hujjojinsa, a iya samun inda yayi daidai da inda ya yi kuskure, sannan a yanke hukunci. Amma nan take, kamar komai, da zarar kowanne irin zargi ya ɓulla, nan take sai mu rabe gida biyu, masu goyon baya da masu suka. Kowanne ɓangare na kare muradinsa kawai.
To, amma fa maganar haye kuɗaɗen da aka nufi aikin addini da su, ba sabon abu ba ne a Izala, domin an gina akidar da yada ta ne ta hanyar amfani da kudaden gwamnati wanda ake bai wa malamai da masallatai tsawon sama da shekaru hamsin a faɗin duniya daga ƙasar Saudiya. Kuma ina kyautata zato, idan ka cire Malam Abubakar Gumi, ba na jin akwai wani malamin Izala da tsira daga irin wannan zargi, domin kowa ya shaida cewa sanda ya ci gasar King Abdul’Aziz ta Riyal 250,000 an ga yadda ya rabar da su, ballantana kuɗin masallaci. Kuma mun ga yadda ya mayarwa da Isyaka Rabiu zakkar Naira miliyan biyu da hujjar cewa, ya raba ta a Kano mana inda yake zaune, tun da da akwai dubban mabuƙata.
Ko a zahiri ka duba yadda a yanzu malamai ke hawa manyan motoci, suke tamfatsa gidaje da sanya ɗanyun shaddodi da kwalliya (kamar yadda a kwanan nan Sule Lamiɗo ya kalli idon Sheikh Sambo Rigacikun ya gaya masa). To ina ake samun waɗannan maƙudan kuɗaɗen?
Ko yanzu yanzu ba sai an jima ba, ba kuma ko a lahira ba, zan iya bayar da shaida a gaban Allah cewa ni ganau ne na yadda wasu malaman Izala ke samun kuɗaɗe ta hanyar danne abubuwa da ake karɓowa daga Saudi Arabiya da sunan addini.
A shekarar 2002, bayan na kammala rubuta littafina akan nazari tsakanin kimiyya da ƙur’ani, sai wani abokina a ‘National Assembly’ ya ce, ya kamata a buga wannan littafi naka a watsa shi a duniya, saboda ƙarancin nazari akan fannin. A wannan yunƙuri nasa, sai ya gabatar da ni ga Babban Darkata na Rabida (Muslim World League) da ke Abuja, wato Dr. Fadoul Khalud, da zummar ko za su taimaka wajen buga littafin.
Dr. Fadoul bayan ya duba littafin sai ya ce ba su da hurumin tallafawa a Abuja, saboda komai daga Saudiya ake ƙididdige musu. Amma idan zan iya, zai ba ni takarda na kai hedikwatar Rabida a Jeddah. Na yi na’am da shawarar, inda ya rubuta min takarda cike da yabon aikin tare da neman Rabida ta buga littafin. Na nemi ‘Entry visa’ ta wata uku na tafi Saudiya. Na je Rabida, inda su ka karɓi takardar da zummar za su duba su gani. Haka na yi ta zirga-zirga a ofishinsu tsawon watanni uku, kullum gobe ka dawo. Ta kai har na saba da jami’in da ke kan maganar takarda ta yadda har gidansa yake gayyata ta. Wata rana mu na ofishinsa wata takardar aiki ta biyo ta ofishinsa zai saka hannu, sai ya ce min ai makarantu ne a garinmu, wato Kano, da ake bai wa wani tallafi na dubban Riyals duk wata saboda gudanarwa. Na duba ‘list’ ɗin gwamman makarantu na allo (ba islamiyya ba) da ke cikin ‘list’ ɗin kuma na riƙe sunayen waɗansu da adireshinsu. Wallahi akwai waɗanda da na dawo Kano babu su, wasun kuma ba su san da wannan tallafi ba.
Bayan na sabunta ‘entry visa’ ta, na je wajen wani babban jami’in ‘Nigerian Consulate’, Mansur Liman, na gaya masa abinda ya kawo ni da yadda suke ta ƙwallo da ni. Sai ya ba ni shawarar cewa, zai haɗa ni da Bashir Aliyu Umar, wanda a lokacin yana karatun ‘Phd’ ɗinsa a Madina ko zai taimaka min. Na je Madina, inda muka sadu da Dr Bashir a cikin masallacin Manzo (SAW) muka tattauna da shi. Bayan ya duba ‘manuscript’ ɗina da takardar Dr. Fadoul, sai ya ce min a gaskiya Malam Ali, duk da wannan aiki naka na da mahimmanci, matsalar mutanen nan ba wani abu wanda wani daga wajen zai zo musu da shi su ɗabbaƙa shi, sai wanda suka tsara wa kansu. Wannan bayani ya gamsar da ni sakamakon yadda mutanen nan suka yi ta ƙwallo da ni ba tare da cewa, ba za su yi ba tsawon watanni. Wannan ya sa na tattara komatsaina, na dawo gida.
Bincike na bayan na dawo ya haska min cewa, mutane a nan ba su san labarin waɗancan maƙudan kuɗaɗe da ake cirewa da sunan wasu makarantun allo a Kano da wasu garuruwa a Arewacin Najeriya ba.
Wajibi ne idan mu na son kauce wa halaka irin wadda Annabi (SAW) ya gargaɗi sahabbai a hadisi na sama, dole sai mun ƙyamaci sata da ‘corruption’ daga duk inda ta fito, walau a manya ko talakawa. Matuƙar za mu ci gaba da bautar ‘elitism’ a Arewa, wallahi halaka ba za ta daina bibiyar mu ba.
Sannan mu sani cewa, akwai wata rana mai zuwa wadda ba ma ka kare wani saboda son zuciya ba, hatta kanka ba za ka iya karewa ba.
Q24:24 “A rãnar da harsunansu da hannãyensu, da ƙafãfunsu suke bãyar da shaida a kansu, game da abin da suka kasance sunã aikatãwa.”
A ƙarshe mu sani cewa, duk al’ummar da ta rasa irinsu Ɗan Bello, tabbas, sata, cin hanci da rashawa da duk wata siga ta zalunci zata ci gaba da dawwama a wannan al’umma.
Malam Ali marubuci ne kuma manazarci a Kano
