Wata Kotun Majistare da ke Karu a Abuja, ta gurfanar da wani mutum da ake zargin ya lakaɗa wa wata mata mai juna biyu har sai da ta yi ɓari.
Mutumin dai ana zarginsa ne da aikata laifukan cin zarafi, da amfani da ƙarfin da ya haddasa wa matar barar da ɗan tayin da ke cikinta.
ɗan Sanda mai gabatar da kara, Olarewaju Osho ya bayyana wa kotun cewa, tun a watan Satumba ne a mutumin ya naushi matar a ciki a tashar motar Karu.
Osho ya ce haka ya janyo wa matar ta yi ɓarin cikinta, kuma laifin ya saɓa wa sashi na 365 na kundin Penal Code.
Sai dai wanda ake zargi ya musanta, inda Alƙalin kotun Hassan Mohammed ya ba da belinsa kan N100,000 tare da gabatar da mai tsaya masa wanda ya mallaki katin shaidar ɗan ƙasa kuma ya mallaki fasfo na tafiye-tafiye zuwa ƙetare.
Baya ga haka, ya umarce shi da ya sanya hannu kan takardar rantsuwar ba zai sake shiga hurumin matar ba.
