Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wata matashiya ’yar Nijeriya mai shekaru 23 mai suna Endurance Daniel ta bayyana irin wahalar da ta sha a tafiyarta zuwa ƙasar Libya, inda ta ce sun kai ga shan fitsarinsu, domin tsira da rayukansu a hamada saboda tsananin ƙishirwa.
Endurance, wacce tana cikin ’yan Nijeriya 182 da ƙungiyar ƙasa da ƙasa kan gudun hijira ta taimakawa wajen dawo da su gida, ta ce, ta yi tafiyar tare da mutane 52 a cikin mota ɗaya, amma bakwai daga cikinsu sun rasu a kan hanya sakamakon yunwa, ƙishirwa da tsananin wahala.
Ta bayyana cewa, an yaudare ta ne tun tana da shekaru 17, inda aka yi mata alƙawarin sama mata aiki yi mai kyau a Libya.
Sai dai da ta isa ƙasar, ta fahimci cewa gaskiyar rayuwa ta bambanta sosai da abin da aka faɗa mata.
“Mun shafe fiye da wata ɗaya a hamada ba tare da ruwa ba.
“A wasu lokuta muna shan fitsarinmu domin mu rayu,” inji ta.
Ta ƙara da cewa daga baya wasu mutane har jini ke fita maimakon fitsari saboda tsananin wahala.
Ta ce wasu daga cikin abokan tafiyarsu sun rasu a hanya, kuma babu yadda za a yi da gawarwakinsu saboda tsananin yanayin da suke ciki.
Endurance ta kuma zargi masu safarar mutane da tilasta wa mata aiki ko kuma karuwanci, tare da hana su komawa gida sai sun biya kuɗin da aka kashe wajen tafiyar.
A ƙarshe, ta yi kira ga matasa da su bincika sosai kafin su yanke shawarar tafiya ƙasashen waje.
