Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Femi Gbajabiamila wanda shine tsohon kakaakin majalisar wakilai ya sanar da cewa babu lokacin aiwatar da rahoton Orunsaye.
Femi ya sanar da haka ne a yayin wata tattaunawa da yayi lokacin da ya kai ziyara hukumar NEITI a Abuja.
Ya ce gwamnatin tarayya na iya ƙoƙarin ganin cewa an samu aiwatar da babu matsala a tare da ita.
In ba mu manta ba, a watan Fabarairu, majalisar zartaswa ta ƙasa a ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta bada umarnin aiwatar da rahoton Orunsaye wanda ya ƙunshi soke wasu ma’aikatun gwamnatin tare da haɗe wasu domin ragewa gwamnatin yawan kuɗin gudanarwa da ta ke kashewa. Gwamnatin Tinubu ta bayar da umarnin aiwatar da wannan rahoto cikin makonni 12 amma yanzu an kai watanni shida an gaza aiwatar wa
