WHO na buƙatar Dala miliyan 87.4 domin yaƙar cutar ƙyandar biri

Spread the love

Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa ta na buƙatar Dala miliyan 87.4 a tsawon wata shida domin yaƙar cutar ƙyandar biri a ƙasashe.

Hukumar ta bayyana cewa wannan kuɗin ta na buƙatar su ne domin auwatar da wasu ayyuka da za su taimaka wajen daƙile yaɗuwar cutar mai mugun haɗari.

Wannan yana ƙunshe ne a cikin jadawalin agajin gaggawa da hukumar ke shirin bayarwa ga ƙasashe da ke fama da annobar.

Hukumar na kira ga masu taimakawa da su kawo agaji domin su fara yaƙin cutar da gaggawa a ƙasashen da ke fama da annobar cutar.

By ukarofi