Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kwamitin Rabon Kuɗaɗen Tarayya (FAAC) ya bayyana cewa, an raba jimillar kuɗin da ya kai Naira Tiriliyan 2.103 ga matakai uku na gwamnati – Tarayya, Jihohi, da ƙananan Hukumomi — a matsayin rabon kuɗin watan Satumba 2025.
Taron raba kuɗin na FAAC ya gudana ne a Abuja a watan Oktoba, inda aka tabbatar da rabon da aka samo daga manyan hanyoyin samun kuɗin shiga — tiriliyan N1.239 daga kuɗin da aka tara ta hanyoyin doka, biliyan N812.593 daga harajin ɓAT, da biliyan N51.684 daga harajin EMTL.
A cewar sanarwar da aka fitar bayan taron, an samu kuɗin shiga gaba ɗaya na tiriliyan N3.054 a watan Satumba, amma aka cire biliyan N116.149 don kuɗin tara haraji, da kuma biliyan N835.005 da aka ware don tallafi, biyan bashi, da tanadin gwamnati.
Kuɗin da aka tara ta hanyoyin doka ya ragu zuwa tiriliyan N2.128, wanda ya yi ƙasa da adadin watan Agusta da N710 biliyan. Sai dai kuma an samu ƙaruwa mai yawa a harajin ɓAT, wanda ya tashi zuwa biliyan N872.63 — ƙaruwa da biliyan N150 idan aka kwatanta da watan da ya gabata.
Daga cikin rabon da aka yi:
Gwamnatin Tarayya ta samu biliyan N711.314
Jihohi sun karɓi biliyan N727.170
Aananan hukumomi sun samu biliyan N529.954
Jihohin da ke samar da mai kuma sun karɓi biliyan N134.956 a matsayin kaso na 13.
FAAC ta ce kuɗin da aka tara daga ɓAT, harajin shigo da kaya, da harajin canja wurin kuɗi sun ƙaru sosai, yayin da kuɗaɗen da ake samu daga harajin kamfanoni (CIT) da harajin kayayyakin CET suka ragu.
Harajin ribar man fetur (PPT) ya tashi kaɗan, amma kuɗaɗen da ake samu daga lasisin man fetur da harajin kayan masarufi sun sauka kaɗan.
Kwamitin ya ƙara da cewa, wannan rabon na watan Satumba ya samo asali ne daga kuɗin shiga na N2.23 tiriliyan daga manyan hanyoyin doka, N812.59 biliyan daga ɓAT, da N51.68 biliyan daga EMTL.
