Na haifi ɗana na farko Ina da shekara 14 – Shina Peters

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Fitaccen mawaƙin Juju na Najeriya, Oluwashina Akanbi Peters, wanda aka fi sani da Sir Shina Peters, ya bayyana yadda rayuwarsa ta fara da wuri sosai, inda ya ce ya zama uba tun yana da shekara 14 kacal.

A wata hirar sa da aka yi da shi a shirin The Honest Bunch Podcast, Shina Peters ya ce ya fara harkar waƙa tun yana da shekara 10, kuma ya cimma manyan nasarori kafin ya kai balaga sosai.

“Na fara sana’ar waƙa ina da shekara 10. Na haifi ɗa na farko ina da 14. Na sayi motata ta farko ina da shekara 13, sannan na gina gidana na farko ina da shekara 16,” inji shi.

Yanzu mai shekara 67, Shina Peters ya ce ba ya ganin zai koma yin sabuwar waƙa saboda yanayin masana’antar waka a yanzu bai dace da shi ba.

“Masoyana suna ta tambaya na yi sabuwar waƙa, amma ba zan iya zuwa studio yanzu ba. Yanayin bai dace ba — ban ma san abin da zan rera ba,” inji shi.

Shina Peters wanda aka san shi da ƙirƙiro salo na Afrojuju, ya kuma bayyana cewa mafi yawan masoyansa suna daga yankin kudu maso gabashin Nujeriya.

“Kashi 65 cikin 100 na masoyana ’yan ƙabilar Ibo ne, ba Yarabawa ba,” inji shi.

Shina Peters yana daga cikin manyan masu tasiri a duniyar waƙa a Nujeriya, wanda ya shahara da rera waƙoƙi masu kuzari da haɗa salon Juju da Afrobeat, abin da ya sa har yanzu yake daga cikin fitattun jarumai a tarihin waƙa ta zamani a Nijeriya.

By ukarofi