Harin NDA ya tayar da hazo

*’Yan bindiga sun kashe da sace jami’an soja a Kaduna
*Za a farauto ‘yan ta’addar – Makarantar NDA
*Ina zargin ’yan cikin gida – Babban Hafsan Tsaro
*Ya kamata wannan ya zama silar gamawa da ‘yan bindiga – Janar Kuka-sheka
*An tsara harin ne don a kunyata Buhari – Garba Shehu
*Tsaron Nijeriya ya rikice – ACF
*Buhari ya mayar da martani mai zafi
*Masu lura da CCTV ba bacci suke ba – Hedikwatar Tsaro

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Abin mamaki da baƙin ciki mai kamar almara ya afku a ranar Talatar da ta gabata a wani harin da ‘yan bindiga suka kai a Makarantar Horar da Sojojin Nijeriya (NDA) da ke Kaduna, inda suka kashe jami’an soja biyu, suka yi garkuwa da ɗaya suka jikkata wani wanda a halin yanzu ya ke jinya a asibiti.

Daga cikin waɗanda suka mayar da martini kan harin na NDA baya ga ita kanta makarantar da ta ci alwashin farautar ’yan bindigar, akwai kuma Babban Hafsan Rundunonin Tsaron Nijeriya (CDS), Manjo Janar Lucky Irabor, Gwamnatin Jihar Kaduna, Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) da Kanar Samuel Agbede, wanda ya ga harin ba kawai abin damuwa ba ne har ma da ban tsoro.

‘Yan bindigar sun kutsa cikin makarantar ne da misalin ƙarfe 1:25 na safiyar ranar, inda suka yi ta harbi ba ƙaƙƙautawa sannan suka nufi sashin jami’an don yin awon gaba da ma’aikatan.

Wata majiyar soji ta ce, an kashe jami’ai biyu, an sace ɗaya, wani da ya jikkata a harin yana karɓar magani a asibitin makarantar yayin da aka sace wasu biyu a harin.

Majiyar ta ƙara da cewa, “a ranar 24 ga Agusta, 2021, da misalin ƙarfe 0125 na dare, ‘yan bindiga da yawansu sun kai hari kan NDA, Afaka, kuma sun yi garkuwa da jami’i ɗaya; Manjo Datong, yayin da laftanar Cdr Wulah da Laftanar CM Okoronwo an harbe su har lahira.

“Laftanar Onah ya samu rauni a harbin bindiga kuma a halin yanzu yana karɓar magani a asibitin sa da ke NDA.”

Da ya ke bayanin yadda ‘yan bindigar suka shiga makarantar, wata majiya ta ce, “sun siɗaɗo ne cikin shiru, ta ɓangaren makarantar inda muka yi waya da shinge kuma ba a yi mana katanga mai kyau ba. Abin takaici, babu sojoji a bakin aikin tsaro a wurin. Don haka, ‘yan bindigar suka samu damar kutsawa ciki inda jami’an suke sannan suka samu uku daga cikinsu. A lokacin da suka harbe ɗaya daga cikin jami’an ne kowa ya farka, kuma kafin mu sani, sun yi hanyar su ta waje sun gudu. Harin babban mari ne a fuskar mu. Ta yaya za mu yarda da hakan? Sun riga sun san babu kowa a bakin aiki inda suka samu damar kutsawa ta wannan hanyar.”

Sai dai, an samu cewa ƙarar harbin da ‘yan bindigar ke yi ya sanar da sojojin NDA ta tawagar ‘Quick Response Team’, waɗanda suka isa wurin, amma ba su samu nasarar kuɓutar da jami’in da aka yi garkuwa da shi ba saboda tuni ‘yan bindigan suka tafi tare da wanda shi.

A cewar majiyar, hukumomin makarantar za su gurfanar da wasu sojoji kotu saboda gaza tabbatar da tsaro a yankin.

Da ya ke mayar da martani game da harin, Bashir Jajira, kakakin makarantar, a cikin wata sanarwa ya kuma yi bayanin yadda aka lalata tsarin tsaro a cibiyar.

Ya ce, “Tsarin tsaro na Kwalejin Tsaro ta Nijeriya ya yi ha]ari da sanyin safiyar yau (ranar Talata) daga wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba wa]anda suka shiga cikin mazaunin cikin Kwalejin da ke Afaka. A yayin wannan abin takaici, mun rasa ma’aikata biyu kuma an sace ɗaya.

Za a farauto ‘yan ta’addar – NDA:

Makarantar tare da haɗin gwiwar Rundunar Sojin Nijeriya na ‘1 Division’ da Rundunar Horar da Sojojin Sama da sauran hukumomin tsaro a jihar Kaduna, tun daga lokacin ta fara farautar ‘yan bindigar da ba a san ko su waye ba a cikin yankin baki ɗaya, da nufin bin diddigin su da kuɓutar da ma’aikatan da aka sace.

Hukumar Makarantar ta NDA ta ce, “al’ummar Makarantar NDA da kadet suna cikin ƙoshin lafiya. Mu na tabbatar wa da jama’a cewa nan ba da jimawa ba za a kamo wannan ‘yan bindigar da ba a san ko su waye ba kuma za a ceto ma’aikatan da aka sace.”

Ina zargin ’yan cikin gida – Babban Hafsan Tsaro:

Shi ma da yake mayar da martani kan harin, Babban Hafsan Tsaro, Manjo Janar Lucky Irabor, ya ce, lamarin ya tayar da hankali, ya ƙara da cewa, sojoji suna duba cikinsa da tsananin sa ido.

Lucky Irabor

Manjo Janar Irabor, wanda bai yi watsi da tunanin cewa kawai haɗin baki da ‘yan ciki ba, ya ce, hukumomin soji za su gano tushen harin.

Martanin nasa ya zo ne a wani zaman tattaunawa na kwana ɗaya tare da manyan hafsoshin soji da suka yi ritaya daga shiyyar Arewa maso Gabas a Birged na 23 da ke Yola, jihar Adamawa.

Babu inda ke da sauran tsaro a Nijeriya yanzu, ‘yan bindiga suna da cikakken iko – A~M Ararile (Mai ritaya):
A martanin da ya mayar, Air Vice Marshall Lucky Ararile (mai ritaya), Ovie na masarautar Umiagwa a jihar Delta, ya ce, “Harin ba-zata da ‘yan bindigar suka kai wa NDA, kashe sojoji da yin garkuwa da wani sojin ya nuna cewa babu inda ke da tsaro yanzu a Nijeriya. Ya nuna cewa ‘yan bindigar suna da cikakken iko.

“Ba mu da tabbacin cewa yanzu Fadar Shugaban ƙasa ko wani sashe na soja yana  da tsaro kuma. Dole ne gwamnati ta magance waɗannan ‘yan bindigar ko duk abin da suka kira kansu da muhimmancin da ya cancanta. Waɗannan abin kunya sun yi yawa.”

*Ya kamata wannan ya zama silar gamawa da ‘yan bindiga – Janar Kuka-sheka:

Haka zalika, Birgediya Janar Sani Usman Kuka-sheka (mai ritaya), tsohon Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojojin Nijeriya, ya ce, “Abin damuwa ne matuƙa. Na yi imani wannan ya kamata ya zama juyi a cikin yaƙar ‘yan bindiga da kuma waɗannan miyagun laifuka. Amma ina tsammanin ‘yan bindiga sun yi babban kuskure. Sun tsallaka layin da za su yi nadama.”

Kuka sheka

“Na yi matuƙar farin ciki cewa dukkan hannaye suna kan wannan batun. Kodayake ba ni da cikakken bayanai, amma ina tsammanin sojoji za su mayar da martani mai zafi yadda ya dace. Na ji cewa CDS da shugabannin hukumar sun ziyarci makarantar. Wannan lamari ne mai tayar da hankali, da gaske yana da tayar da hankali amma na tabbata game da iyawa da ƙarfin sojoji don magance lamarin.”
A nasa martanin, wani ƙwararre kan harkar tsaro, Manjo Bone Efoziem (mai ritaya), ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gyara lamarin domin kaucewa yanayin da ke faruwa a Afghanistan, yana mai bayyana harin a matsayin abin kunya.

Gwamnatin Kaduna ta yi tir da harin:

Har ila yau, harin ya tayar da hankali, gwamnatin jihar Kaduna ta yi kira ga ‘yan ƙasa da su ba da bayanan sirri ga sojoji da hukumomin tsaro a yaƙin da ake yi da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai

Kwamishinan ma’aikatar tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, a cikin wata sanarwa ya ce, “Kasancewa mai masaukin kwalejin kuma abokin tarayya a fannoni da yawa na tsaro da ci gaban ƙasa, an yi wa Gwamna Nasir El-Rufai bayanin lamarin, kuma a madadin gwamnati da Jama’ar jihar Kaduna, sun yi addu’ar Allah ya jiƙan ma’aikatan da suka rasa rayukansu.

“Gwamnan yana isar da tausayawa ga Kwalejin, da kuma iyalai na ma’aikatan, sannan kuma yana matuƙar nuna damuwa ga dangin jami’in da aka sace. Bugu da ƙari, gwamnatin jihar Kaduna ta miƙa haɗin kai mara iyaka ga Sojojin Nijeriya da dukkan hukumomin tsaro da ke yin sadaukarwa mai yawa ta fuskoki daban-daban,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, “Don haka gwamnati ta yi kira ga mutanen kirki na jihar da su ba da sahihan bayanai ga sojoji da hukumomin tsaro a ya}in da ake yi da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane, a cikin jihar da ma bayanta. A nata ɓangaren, gwamnatin jihar Kaduna za ta ci gaba da ɗaukar matakan da ake ganin suna da muhimmanci a yaƙin da ake yi da masu fashi a faɗin jihar.”

Tsaron Nijeriya ya rikice – ACF:

A halin da ake ciki, ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta bayyana kaduwa game da harin da aka kai Cibiyar Horar da Sojojin Nijeriya (NDA).

ACF ta ce, mamaye da lalata kamfanin inda ake samar da dukkan hafsoshin sojin Nijeriya, wata manuniya ce cewa tsarin tsaron ƙasa na Nijeriya yana tafiya a kan kayar baya.

Shugaba Buhari ya mayar da martani mai zafi game da harin:

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, ya mayar da martani kan harin da ‘yan bindiga suka kai a Cibiyar Horar da Sojoji (NDA) da ke Kaduna.


Da yake mayar da martani kan lamarin, Shugaban ya yi ta’aziyya ga iyalan mamacin, inda ya bayyana cewa harin ya zo ne a daidai lokacin da sojoji suka sanya ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, da sauran ire-iren masu aikata laifuka karan tsana.

Shugaba Buhari

A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina, Shugaban ya sha alwashin cewa harin ba zai rage wa sojojin ƙarfi ba amma zai ƙara masu caji wajen kawo ƙarshen aikata laifuka a ƙasar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Harin da aka ƙaddamar a Cibiyar Horar da Sojoji (NDA) a ranar Talata, maimakon jefa wani abin birgewa cikin kwarin gwiwa na Sojojinmu kamar yadda aka yi niyya, za su ƙara azama kan kawo ƙarshen yanke hukunci mai muhimmanci, cin hanci da rashawa a ƙasar.”

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce, “lura cewa harin, wanda ya yi sanadiyar asarar rayuka, ya zo ne a daidai lokacin da sojoji suka sanya wa masu tayar da ƙayar baya, masu garkuwa da mutane, da sauran ire-iren masu aikata miyagun laifuka karan tsana. Wannan mummunan aikin zai gaggauta kawar da mugunta gaba ɗaya a cikin ladabi, wanda mambobin rundunar Sojin ke da ƙuduri don aiwatarwa cikin ƙanƙanin lokaci.”

An tsara harin ne don a kunyata Buhari – Garba Shehu:

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban ƙasa, ya bayyana cewa, harin da aka kai a Cibiyar Horar da Sojoji (NDA) na iya zama wata dabara don kunyata gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Garba Shehu

Da yake mayar da martani kan lamarin a ranar Laraba, Shehu, a cikin wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels, ya ce, fadar shugaban ƙasa na sa ran sojoji za su yi bincike sosai tare da bayyana abin da ya faru.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar, wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin baƙin ciki da rashin sa’a, ya bayyana cewa, ana duba cikin lamarin sosai don sanin haƙiƙann abin da a haifar da lamarin.

Ya ce, mai yiwuwa ne waɗanda ke son kunyata wannan gwamnati ta yanzu, su tsara wannan lamarin, sakamakon manyan nasarori da sojoji suka samu a yaƙin da ake yi da masu tayar da ƙayar baya da ‘yan bindiga. Shehu ya ce, lamarin na iya kasancewa yana da nasaba da siyasa.

Masu lura da CCTV ba bacci suke ba – Hedikwatar Tsaro:

A wani ɓangaren kuma, Hedkwatar Tsaron Nijeriya ta ce, ma’aikatanta da ke kula da ɗakin sanya idanu (CCTV) na NDA sun kasance a farke lokacin da ‘yan bindigar suka mamaye NDA ɗin a Kaduna, saɓanin rahotannin farko da ke nuni da cewa, bacci suke yi a lokacin harin.

Haka zalika, a cikin sanarwar ta na musantawa a ranar Laraba, Hedikwatar ta ce, zargin ba gaskiya bane.

“Wata}ila yana da muhimmanci a ambaci cewa, AFN a matsayin ƙwararrun sojoji sun ƙunshi ƙwararrun ma’aikata waɗanda aka sadaukar da su ga ayyukan kare rayuka da dukiyoyin dukkan ‘yan Nijeriya,” in ji sanarwar da Benjamin Sawyerr, kakakin Hedikwatar ya fitar.

“Bari na yi amfani da wannan damar, don sake nanata cewa, hukumomin NDA su na yin aiki da umarnin Babban Hafsan Tsaro sun kuma kafa kwamitin bincike, don gano sanadiyyar dalilan da suka sa aka samu taɓarɓarewar tsaro tare da niyyar yin hukunci ga duk wani ma’aikacin da aka samu da laifi, don hana faruwar hakan nan gaba.”