Da Ɗumi-ɗuminsa: ‘Yan bindiga sun kashe ɗan gidan Sanata Ibn Na Allah, Captain Abdulkarim Na Allah a Kaduna

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a Kaduna, sun kashe Captain Abdulkarim Bala Na Allah, wanda shi ne babban ɗan Sanata Bala Ibn Na Allah, a gidansa da ke umar Gwandu a Malali, Kaduna.

Za a yi jana’izar marigayin a maƙabartar Unguwar Sarki Kaduna.

Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda inda wasu ‘yan bindiga suka halaka Major Christopher Dator bayan sun yi garkuwa da shi sakamakon harin da suka kai makarantar horas da manyan jami’an sojoji (NDA) a Kaduna.

Cikakken rahoton na nan tafe.