Kwanan nan, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta ce kawo yanzu ƙasar nan ta samu adadin mutane 871 da aka tabbatar sun kamu da cutar zazzaɓin Lassa inda mutane 162 suka mutu sannan adadin waɗanda suka kamu da cutar ya haura zuwa kashi 18.6 cikin ɗari.
Yana da kyau a lura cewa zazzaɓin Lassa ya kashe ‘yan Nijeriya 883 a cikin shekaru biyar kacal, amma duk watan Janairu idan lokacin rani ya zo, ana mamakin ɓarkewar cutar.
Shekaru da yawa, waɗannan jihohi biyar sun ta fama da wannan cuta. Ondo ce ke da kashi 33 bisa ɗari, Bauchi kashi 23, Edo kashi 17, Taraba kashi 14, sai Ebonyi kashi 3. Tare, waɗannan jihohin suna wakiltar kashi 90 cikin ɗari na duk cututtukan da aka tabbatar.
Cutar Lassa, wadda ta samo asali daga jikin ɓeraye da kuma ke janyo tsananin zazzaɓi, na ci gaba da yaɗuwa a yammacin Afrika, inda Nujeriya ta kasance cikin jerin ƙasashe da ake samun ƙaruwar masu cutar.
Cutar, mai haddasa tsananin zazzaɓi mai ɓullar jini a jiki, ba ta da riga-kafi da aka amince da shi da kuma cibiyoyin yin gwaji, abin da ke janyo tarnaki wajen magance ta.
Waɗanda suka warke daga cutar na fuskantar ciwuka na tsawon lokaci da kuma tsangwama.
ƙwararru sun ce sauyin yanayi da kuma cunkoson al’umma a wuri guda, na cikin abubuwan da ke ta’azzara cutar – yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ganin an samar da riga-kafinta.
Talla
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce cutar Lassa na iya zama annoba a duniya a yanzu, inda ƙasashe kamar Birtaniya da Amurka suka ayyana ta a matsayin cuta mai haɗari.
Yayin da yawancin mutane da suka kamu da cutar ke ganin ƙananan alamomi a yawan lokuta, tana kasancewa kamar Ebola idan ta yi tsanani, abin da ke janyo barazana ga rayuwar mutum. Mata masu juna biyu da kuma jami’an lafiya ne suka fi shiga haɗari.
Cutar wadda aka fara gano ta a Nijeriya a 1960, ta fi shafar ƙasashen Nijeriya da Guinea da Laberiya da kuma Saliyo. Sai dai, ana ci gaba da samun masu kamuwa da cutar a sauran ƙasashen yammacin Afrika.
Tun watan Janairun wannan shekara, Nijeriya ta kasance tana fama da ɓarkewar cutar Lassa. Jihar Ondo kaɗai ta ruwaito samun mutum 100 da suka kamu da ita. Yayin da sama da mutum 500 suka kamu da cutar a ƙasar baki ɗaya – inda aka ruwaito mutuwar mutum 90.
Ana samun cutar ne daga nau’in wasu ɓeraye da ake kira ‘multimammet rats’ a Turance. Sun kasance suna shiga cikin gidaje da kuma lalata abinci da aka dafa. a ƙauyuka kuma, ɓerayen na amfani da barin ɗakuna a buɗe wajen afkawa cikin abinci.
Mutanen da suka mutu sakamakon cutar Lassa sun kai kashi ɗaya, a cewar WHO, sai dai alkaluman za su iya fin haka lokacin ɓarkewarta zuwa kashi 20.
Ana wahala wajen gano cutar idan ta kama mutum da farko, inda take kama da maleriya da kuma cutar dengue.
Rashin yin gwaji a-kai a-kai na nufin ana dogaro da cibiyoyin yin gwaji, waɗanda ake fama da ƙarancinsu a yankunan da ake fama da cutar.
A yanzu, ana samun ɓarkewar cutar a kowace shekara, abin da ke janyo damuwa kan sauyin yanayi.
A Nijeriya, ƙara ƙaimi wajen saka ido ya janyo samun ƙaruwar masu kamuwa da cutar. ƙasar na kuma ƙarfafa cibiyoyin kula da masu cutar.
Ministan Lafiyar na Nijeriya, Farfesa Muhammed Ali Pate ya ce Nijeriya na haɗin gwiwa wajen samar da riga-kafin cutar da kuma inganta kariyar jami’an lafiya da ke bakin aiki.
Ana aikin gwada ɗaya daga cikin alluran a Nijeriya da Ghana da kuma Laberiya.
