A wani rahoto na bincike daga Reuters, an ruwaito cewa dalar Amurka na fuskantar matsin lamba mai ɗorewa, musamman daga manufofin saukin riba (interest rate cuts) da Juya ra’ayin masu zuba jari zuwa wasu kuɗaɗe da kadarorin da suka fi aminci kamar zinariya.
Poll ɗin da masana musayar kuɗi suka yi ya nuna cewa dalar za ta kasance mai rauni a cikin watanni 3, 6, zuwa shekara guda masu zuwa. Hakan ya samo asali ne daga haɓakar gibin kuɗin gwamnatin Amurka, saɓanin ra’ayin cewa Babban Bankin Tarayya (Fed) na iya rasa cikakken iko ko yanke rahusa a kan riba.
An lura cewa euro ya riga ya tashi kusan 13% a kan dalar a shekarar nan, yayin da sauran kuɗaɗe kamar Yen da kuɗaɗen Australiya da New Zealand suna samun ƙarfi. Zinariya kuma ya karu fiye da kashi 47%.
Masana tattalin arziki sun faɗi cewa girman bashin gwamnati da ƙarancin samun bayanai idan gwamnati ta dakatar da aiki (shutdown) na ƙara dagula hasashen masu zuba jari game da makomar dalar. Wannan ya sa ra’ayin rage riba ya zama karami ga masu la’akari da hada-hadar kasuwanci.
