Jane Goodall: Duniya ta yi rashin babbar masaniyar kariyar muhalli

Spread the love

Jane Goodall, fitacciyar masanin birrai kuma shugabar ƙungiyoyin kare halittu, ta rasu a ranar 1 Oktoba, 2025, tana da shekaru 91. Marigaya Goodall ta rasu ne sakamakon dalilai na gajiya, yayin da take cikin yawon jawabi a California, Amurka, kamar yadda Jane Goodall Institute, da kuma hundreds of media outlets na duniya suka ruwaito. 

Ta shahara sosai saboda bincikenta a filin Gombe a Tanzaniya tun daga 1960, inda ta fara nazarin halayyar chimpanzees, musamman yadda suke yin amfani da kayan aiki (tools) da al’adarsu. Ta jawo hankalin duniya cewa irin waɗannan halayen babu bambanci sosai tsakanin dabbobi da mutane. 

A shekarun baya Goodall ta mayar da hankali sosai wajen wayar da kan al’umma kan muhalli, sauyin yanayi, da kiyaye gandun daji. Ta kafa Roots & Shoots, shirin da ke koyar da matasa tasirin su wajen kare muhalli. Har zuwa karshen rayuwarta, tana yin jawabi a wurare da dama na ƙarfafa matasa da jami’oin gwamnati su ɗauki matakin kare halittu.

By ukarofi