Hauhawar farashin kaya ya ragu da kashi 22.97 a Mayu, inji NBS

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) a ranar Litinin ta ce hauhawar farashin kayayyaki ya ragu zuwa kashi 22.97 a watan Mayun 2025 daga kashi 23.71 da aka samu a watan Afrilun 2025.

Babban jami’in ƙididdiga na tarayya, Prince Adeyemi Adeniran ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja.

Ya ce, “Hauhawar farashin kayayyaki a watan Mayun 2025 ya ragu zuwa kashi 22.97 bisa ɗari idan aka kwatanta da na Afrilu na 2025 na kashi 23.71 cikin ɗari. Wannan yana nuna raguwar 0.74 daga Afrilu 2025.”

Ya ce, a duk wata, hauhawar farashin kayayyaki a watan Mayun 2025 ya kan kai kashi 1.53, wanda ya yi ƙasa da kashi 0.33 bisa ɗari idan aka kwatanta da na watan Afrilun 2025 (kashi 1.86).

A cewarsa, gudunmawar da aka bayar ga farashin kayayyaki a matakin sashe, manyan abubuwa uku da suka bayar da gudunmawar hauhawar farashin kayayyaki sun haɗa da abinci da abubuwan sha: kashi 9.20 cikin 100, abinci da gidaje: 2.97 bisa zari, da Sufuri: 2.45 bisa ɗari; yayin da mafi ƙanƙanta masu ba da gudunmawa sune nishazi, wasanni, da al’adu: 0.07 bisa ɗari, abubuwan barasa, sigari, da kwayoyi: 0.09 bisa ɗari, da inshora da ayyukan kuɗi: 0.11 bisa ɗari.

Ya ce a duk wata, hauhawar farashin kayan abinci a watan Mayun 2025 ya kai kashi 2.19, wanda ya ƙaru da kashi 0.13 bisa ɗari idan aka kwatanta da Afrilun 2025 (kashi 2.06).

Shugaban na NBS ya ce ana iya danganta ƙaruwar farashin kayayyaki da suka haɗa da doya, rogo, garin masara, attaruhu, dankali, da dai sauransu.

Dangane da hauhawar farashin kayayyaki, wanda ya keɓanta farashin amfanin gona da makamashi, NBS ta ce ya kai kashi 22.28 cikin 100 a watan Mayun 2025 a duk shekara.

Ya ce a duk wata-wata, ainihin hauhawar farashin kayayyaki ya kasance kashi 1.10 cikin 100 a watan Mayun 2025, ya ragu da kashi 0.24 daga Afrilu 2025 (kashi 1.34).

By ukarofi