Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
’Yan kasuwar man fetur sun ƙara farashin farashin fetur a gidajen mai a ci gaba da gasa da matatar man Dangote.
Bayanan da wannan jarida ta tattara daga Petroleumprice.ng a ranar Talata ta nuna cewa gidajen man fetur guda bakwai sun ƙara farashin da ya kai kashi 1.45 zuwa 2.90 tsakanin 11 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuni.
Canje-canjen da aka samu a manyan gidajen mai na Legas tsakanin 11 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuni, 2025, sun nuna yadda farashin man fetur ya hauhawa:
Aiteo: N825 – N840 (1.82 ya ƙaru)
Nipco: N827 – N845 (ƙara 2.18)
Menj: N826 – N850 (ƙara 2.90)
First Royal: N826 – N838 (ƙara 1.45)
Emadeb: N827 – N845 (ƙara 2.18)
Pinnacle: N829 – N845 (ƙara 1.93)
Swift: N830 – N845 (ƙara 1.81)
A ɗaya hannun kuma, matatar Dangote ta nuna jajircewarta ta hanyar kiyaye tsohon farshin sari akan N835 kowace lita.
Wannan ci gaban ya biyo bayan shirin matatar man Dangote na fara rabon man fetur da suka haɗa da iskar gas, daga ranar 15 ga watan Agusta.
Shugaban ƙungiyar Masu Kayayyakin Man Fetur ta Nujeriya (PETROAN), Billy Gillis-Harry, ya bayyana cewa ƙungiyar na gudanar da taruka tun bayan da matatar man ta bayyana shirin fara rabon mai a faɗin ƙasar.
A yayin da Gillis-Harry ya bayyana a matsayin baƙo a shirin gidan Talabijin na Channels na ‘The Morning Brief’ a ranar Talata, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da masu kula da harkokin man fetur da suka haɗa Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur (NMDPRA), da su dakatar da ayyukan faɗaɗa matatar Dangote.
“Idan kamfani ɗaya mai girma kamar na ɗan uwanmu (Aliko Dangote) zai iya yin duk wannan, tabbas zai iya gurgunta mana kasuwanci,” inji shi.
