Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya tabbatar wa gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno da magoya bayansa da suka biyo shi cikin jam’iyyar APC mai mulki cewa ba za su yi nadamar zama jam’iyyar da ke mulki ba.
Ya ce shugaban jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci musamman da ya sanar da Gwamnan cewa APC za ta zama gidan sa, kuma babu wanda zai wulakanta shi, ko kuma tambayar matsayinsa a jam’iyyar.
Sanata Shettima ya bayyana haka a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, inda ya wakilci shugaban ƙasa a yayin liyafar da Gwamna Umo Eno ya kira.
Da yake jawabi ga ɗimbin magoya bayan jam’iyyar APC da suka yi dafifi.
Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana ubangidan nasa, Tinubu a matsayin wanda ya gina gada kuma mai bin tafarkin dimokuraɗiyya wanda ya sadaukar da dukiyarsa don ci gaba da fafutukar kare dimokuraɗiyyar ƙasa.
Da yake tunawa da irin rawar da shugaba Tinubu ya taka wajen ɗorewar dimukraɗiyya a Najeriya.
“Mai girma shugaban ƙasa ya buƙaci a tabbatar maka cewa: babu wanda rike ka bare, wannan jam’iyya ce da ka zama ɗan gida, ba za a wulakanta ku ba, ba za a yashe ku ba, mu ‘yan uwanku ne.
Mataimakin shugaban ƙasan ya kuma yi wa sabbin ‘yan jam’iyyar APC albishir cewa jam’iyyar APC mai mulki ta ginu a kan kima da daraja , shi ya sa ta ci gaba da zama jam’iyyar shekaru masu tsawo.
Don haka ne ma tayi tsawon shekaru har goma cur, duk da ana ɗan samun rashin jituwa a nan da can amma ta samu cigaba.
A nasa jawabin, Gwamna Eno ya ce ya yanke shawarar komawa jam’iyyar APC ne saboda burinsa na ganin dacewar tsare-tsaren gwamnatin Bola Ahmad Tinibu mai son cigaban ƙasa da dimukraɗiyya.
Ya ce shiga jam’iyyar APC zai taimaka wajen aiwatar da ayyukan samar da ababen more rayuwa a jihar Akwa Ibom, ciki har da aikin tashar ruwa mai zurfi da aka shafe tsawon shekaru talatin ana yi.
Shi ma a nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje, ya bayyana taron jama’a a matsayin abin tsoro, inda ya ce jama’a sun fito ne da son ransu na komawa Gwamna Umo Eno domin sun yi imani da APC.
“Haɗin kan ƙasa yana haifar da ci gaban ƙasa, ci gaban ƙasa yana haifar da haɗin kan ƙasa kuma yana haifar da ci gaban ƙasa,” in ji shi.
A nasa ɓangaren, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana mataimakin shugaban ƙasar a matsayin wanda ya kasance mai tunani da hankali da hangen nesa kuma mutum ne mai gaskiya.


