Daga ALIYU ABDULLAHI GORA II
Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Dikko Umar Raɗɗa.
Mai girma gwamnan jihar Katsina Alhaji Dikko Umar Radda, ina yi maka barka da Sallah da fatan alheri. Muna kara jinjina maka bisa namijin kokarin da ka ke yi na wanzar da zaman lafiya a fadin jihar Katsina. Wannan, budadden korafi ne daga al’ummar garin Gora II.
Gora II gari ne mafi girma a karamar hukumar Safana. Mu ke da kasuwa mafi girma a karamar hukumar Safana. Mun shahara a bangaren harkokin noma da kiwo da kasuwanci. Al’ummar garin Gora II mutane ne masu son zaman lafiya a ko da yaushe. Wannan shi ya sa duk kauyukan da ke zagaye da garin su ka yi hijira zuwa Gora II domin ci-gaba da ruyuwa saboda fitinar ‘yan bindiga.
Ya mai girma gwamna, tun daga ranar da aka kwashe Sojojin da ke ba mu tsaro muka shiga tasku. Ba mu barci da ido biyu, harkokin kasuwanci da noma da kiwo sun tsaya cak. Hada-Hadar yau da kullum ta gagagri jama’a. Tuni mutane da dama sun fara hijira daga garin zuwa manyan birane don tsira da rayukan su. Ina da tabbacin cewa ba ka da masaniya a kan abin da ke faruwa.
Bayan an kwashe sojojin, an samu wasu tsirarun Fulani da ke sintiri a garin wai da sunan ba mutane kariya. Ko a ruguntsumin bikin Babbar Sallan nan mun ga tashin hankali.
Mutanen nan sun shigo gari da izza su na wulakanta mutane. Kiri-kiri sai sun zabi budurwa su damkar mata Nono a gaban mutane kuma ba wanda ya isa ya ce uffan. Ya mai girma, yanzu al’ummar garin Gora II ba su da gata sai Allah sai kai.
Ni haifaffen garin Gora II ne, amma ni da ire-ire na zuwa garin ma ya gagare mu. Don Allah ka tausaya ka sa a maida mana sojojin nan mu samu sukuni. Idan ba a yi gaugawar daukar mataki ba, ina mai tabbatar maka ‘yan bindiga sai sun maida garin nan Kufai.
Da fatan za ka dubi wannan korafi da idon basira. Allah ya kara maka hikima da basirar mulkar al’ummar jihar Katsina. Allah ya tsawaita rayuwar ka cikin aminci. Mun gode.
Aliyu Gora II ma’aikaci ne a gidan rediyon Liberty da ke Kaduna
