Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta sanar da cewa, hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu tsawon watanni biyu a jere, daga kashi 34.19 a watan Yuni zuwa kashi 33.40 a watan Yuli, kuma yanzu haka ya kai kashi 32.15 a watan Agusta.
Dangane da rahoton ƙididdigar farashin kayayyaki da ofishin ya fitar, an samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki zuwa kashi 32.15 cikin 100 a watan Agustan 2024, yayin da hauhawar farashin kayayyakin abinci ya kai kashi 37.52 a cikin wannan wata.
“Farashin watan Agusta 2024 ya nuna raguwar maki 1.25 idan aka kwatanta da farashin watan Yulin 2024,” inji NBS.
“Duk da haka, a kowace shekara, hauhawar farashin ya kan kai kashi 6.35 sama da adadin da aka rubuta a watan Agusta 2023 (kashi 25.80).
NBS ta ce hauhawar farashin kayan abinci a watan Agustan 2024 ya kai kashi 37.52 a duk shekara, wanda ya kai kashi 8.18 idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Agustan 2023 (kashi 29.34).
Ta ce, hauhawar farashin kayan abinci a kowace shekara ya kan faru ne a sanadiyyar hauhawar farashin kayayyaki kamar, burodi, masara, hatsi, dankalin Turawa, dawa, doya, dabino, man gyaɗa, kayan lambu, da sauransu
