Majalisa ta umarci bankin GTbank ya biya harajin VAT na Remita daga 2015 zuwa 2022

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Majalisar Wakilai ta buƙaci bankin Guaranty Trust, GTB, da ya tura harajin ɓAT na Remita tsakanin shekarar 2015 zuwa 2022 zuwa asusun Gwamnatin Tarayya.

Shugaban kwamitin kula da asusun gwamnati, PAC, na majalisar wakilai, Bamidele Salam (PDP ta Osun), ya ba da wannan umarnin ne a ranar Alhamis yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan zarge-zargen ƙin biya kuɗaɗen shiga ta hanyar REMITA.

Kwamitin yana kuma binciken rashin bin ƙa’idar aiki da sauran abubuwan da suka shafi harkar bankin.

Remita fasaha ce ta kuɗi da Gwamnatin Tarayya ke amfani da ita don tattara kuɗaɗen shiga daga hukumomin gwamnati zuwa cikin Asusun Baitul Malin ƙasa, TSA.

Umurnin na Bamidele ya biyo bayan shawarar da kwamitin ya ɗauka na bai ɗaya bayan ya binciki bayanan tare da sauraron shugabannin bankin.

Tun da farko, Babban Darakta na GTB, Ahmed Liman, ya ce bankin ba ya fitar da ɓAT na tsawon shekaru takwas.

Ya ce, bankin ya yi imanin cewa Remita ta cire ɓAT kafin ta raba kwamitocin da bankin.

“Mun yi imanin cewa Remita na da alhakin raba kuɗaɗen hukumar tsakanin masu karɓar albashi.

“A tunaninmu, Remita ya yi abin da ake buƙata kafin raba kuɗaɗen tsakanin ɓangarori,” inji shi.

Babban daraktan ya ce bankin na karbar kashi 0.75 bisa 100 ga duk masu biyan kuɗin da suka yi amfani da tsarin Remita.

Ya ƙara da cewa, bankin ya karɓi Naira 254, 489, 013 daga hannun Akanta Janar ta hannun Remita a shekarar 2018.

Sauran bankunan da kwamitin ke ci gaba da binciken bayanansu sun haɗa da Keystone, Zenith, Sterling, Polaris, FCMB, Ecobank da Wema.

By ukarofi