Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta fara jigilar abinci zuwa Maiduguri

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar Sojin Saman Nijeriya, NAF, ta ce ta fara jigilar kayan tallafin abinci zuwa birnin Maiduguri sakamakon ambaliyar da ta shafi mutum fiye da miliyan biyu.

Tallafin kayan abincin dai ya samu ne daga hukumar hana fasaƙauri ta Nijeriya, Kwastom.

Rundunar sojin saman ta ce a ranar Asabar ta fara kai kayan Maiduguri inda jiragenta suka kai shinkafa buhu 300 masu nauyin kilogram 50 kowanne, a zangon farko.

Rundunar ta kuma ƙara da cewa tuni da ma ta fara ayyukan bayar da magani ga waɗanda ba su da lafiya.

Mataimakin daraktan hulɗa da jama’a da yaɗa labarai na NAF, Kyaftin Kabir Ali ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Abuja.

Ali ya ce, aikin jigilar kayan tallafin abincin ya cika aikin da NAF ta kafa na ba da agajin soji ga hukumomin farar hula (MACA).

Ya ce, kayayyakin da ake kai wa ta jirgin, hukumar kwastam ta Nkjeriya ce ta bayar da gudunmuwarsu, da nufin rage radadin bala’in da ambaliyar ruwa ta haifar, wanda ya kawo cikas ga rayuwar yau da kullum, da lalata dukiyoyi, da kuma raba miliyoyin da muhallan su.

A cewarsa, jirgin wanda ya fara jigila a ranar 14 ga watan Satumba, ya samu kaso na farko na kayan agaji na buhu 300 na shinkafa mai nauyin kilogiram 50, kuma an yi nasarar isar da su zuwa sansanin NAF da ke Maiduguri ta jirgin NAF C-130 Hercules.

“Kwamandan Rundunar Sojan Sama, Air Commodore UU Idris, ya karɓi kayayyakin, ya kuma miƙa su ga Kwamishinan Ma’aikatun Gwamnati da Ayyuka na Musamman, Alhaji Tukur Ibrahim, wanda ya samu rakiyar Kwanturolan Hukumar Kwastam ta Nijeriya, MD Malah.

“Haka zalika, an kuma yi amfani da manyan motocin ɗaukar kaya da NAF ta bayar wajen jigilar kayayyakin zuwa gidan gwamnatin jihar Borno domin ci gaba da rabawa.

Bugu da ƙari, NAF ta ƙaddamar da wani shiri na wayar da kan jama’a don tallafawa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa.

“Wannan shiri ya haɗa da samar da magunguna, abinci, da kuma samar da ruwa don taimakawa wajen rage illar ambaliya da kuma magance buƙatun gaggawa na mutanen da abin ya shafa,” inji shi.

A halin da ake ciki kuma, wata tawaga da ta ƙunshi ƙungiyoyi daban-daban a ƙarƙashin Majalisar ɗinkin Duniya, ta isa Maiduguri a ranar Asabar don ziyarar tantance irin ɓarnar da ambaliyar ruwa ta haddasa.

A cikin tawagar akwai ƙungiyoyi masu zaman kansu na ƙasa da ƙasa, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar ɗinkin Duniya na ‘Resident and Humanitarian Coordinator’ a Nijeriya, Mohamed Fall.

Tawagar wacce ta ziyarci sansanoni don yin mu’amala da waɗanda abin ya shafa, sun kuma kai ziyarar nuna goyon baya ga Gwamna Zulum sannan kuma sun yi mu’amala da ‘yan jarida.

Da yake jawabi a kan ƙalubalen ifta’in, Fall ya tabbatar wa gwamnati da al’ummar Borno na goyon bayan Majalisar ɗinkin Duniya, yana mai cewa: “Dukkanmu muna tare da ku cikin tausayawa da haɗin kai kuma za mu yi iya bakin ƙoƙarinmu.

Ya ce hukumar raya ƙasashe ta Majalisar ɗinkin Duniya (UNDP) za ta yi nazari mai zurfi bayan bala’i, duba da kafa shirin farfaɗowa.

Zulum ya fayyace wuraren da ke da buƙatu na gaggawa:

A nasa martanin, Gwamna Zulum ya gode wa tawagar Majalisar ɗinkin Duniya bisa jerin shirye-shiryen da ta ke yi a jihar, yayin da ya tabbatar da aniyar gwamnati ta haɗa kai da su.

Zulum, wanda ya yi magana kan girman ɓarnar da ambaliyar ta yi, ya buƙaci hukumomin Majalisar ɗinkin Duniya da su fara mayar da hankali kan buƙatun gaggawa na waɗanda abin ya shafa kamar abinci, lafiya, matsuguni da saftar ruwa.

Gwamnan ya kuma ce akwai buƙatar a tallafa wa wasu da ke amfani da makarantu a matsayin sansani domin su koma gidajensu cikin ƙanƙanin lokaci domin baiwa yara damar komawa makaranta.

Gwamnan ya ce tare da goyon bayan amintattun abokan aikin sa, gwamnatin sa ba za ta bari afkuwar ambaliyar ta hana ta aiwatar da shirinta na ci gaba ba.

NAN ta ruwaito cewa sama da mutane 414,000 ne suka rasa matsugunansu sakamakon mummunar ambaliyar da ta afku a ranar Talata a Maiduguri.

By ukarofi