LAFIYA UWAR JIKI: Sirrikan abinci guda bakwai

Spread the love

1. Cin ganyayyaki da hatsi na taimakawa wajen daƙile cutuka masu dogon zango a jikin ɗan adam irinsu ciwon zuciya, ciwon sukari da wasu nau’o’in ciwon daji.

2. Cin Kifi na taimaka wa lafiyar zuciya da ta ƙwaƙwalwa. Ya na taimaka wa fahimta da rage haɗarin kamuwa da ciwon zuciya.

3. Yawan yin azumi na taimakawa ƙwayoyin halittar jiki su yi wa kansu garanbawul ko sabis. Saboda haka ba ka buƙatar shan wani jiƙo ko magani dan yiwa Jikinka sabis. Yawaita yin azumi ya wadatar.

4. Shan madarar yoghurt na inganta lafiyar hanji da kuma taimakawa wajen narkar da abinci. Ana hasashen cewa ya na taka rawa wajen rage ciwon damuwa.

5. Shan kayan marmari irinsu inibi da danginsa na taimakawa wajen zuƙe sinadarai da ke saurin tsofar da jiki, karshe su jawo cutuka masu dogon zango. An alaƙanta yawan shan kayan marmari da takawa saurin saukowar tsufa birki.

6. Tsari mai kyau wajen cin abinci mai gina jiki ya na inganta lafiya da gina tsokar jiki. Misali; idan ka na da kifi da nama da ƙwai, to kar ka cinye su lokaci guda. Ka ci ƙwai da safe, nama da rana, sannan kifi da daddare.

7. Shan isasshen ruwa kamar yadda na sha faɗa, ya na da matuƙar alfanu. Ya na ƙara nutsuwa, kuzari da lafiya bakiɗaya. Idan ka na wasa da shan ruwa, to nutsuwar ka da ganewarka da fikirarka na cikin haɗari. A sha ruwa a wuni kamar fiyawota guda shida zuwa sama. 

Na gode.

Naku M. I. Abdullahi

By ukarofi