
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hedikwatar Tsaron Nijeriya DHQ, ta ce sojojin ƙasar za su cigaba da aiki a ƙarƙashin tsarin da ake kai, wato ‘Harmonised Terms and Conditions of Service (HTACOS) duk da hukuncin wata kotun ƙasa da ta bayyana wasu tsare-tsaren da suka saɓa wa dokar ƙasa acikin sharuɗɗansa.
A ranar Talata, Mai Shari’a Emmanuel Subilim na kotun harkokin ƙasa a Abuja, ya rushe tsarin HTACOS da ya shar’anta wa soja yin aiki na tsawon shekaru 15 kafin ya samu cancantar yin murabus ko ritaya.
Kotun ta ce, hakan ya saɓa wa dokar ƴancin ɗan-adam ƙarƙashin kundin dokar ƙasa na 1999.
Hakan na zuwa ne bayan da Laftanal J.A Akerele, wanda ya fara aiki a matsayin sojan Nijeriya a shekarar 2013 ya shigar mata da ƙara akan lamarin.
Ya yi zargin cewa an hana shi ajiye aiki bayan ya nemi hakan sakamakon ƙalubalen da ya ke fuskanta kasancewarsa jami’i, lamarin da ya jefa shi cikin ƙunci.
A yayin hukunci kan al’amarin ne kotun ta bayyana hakan a matsayin bautarwa ta zamani da sunan yi wa ƙasa hidima.
Hukuncin kotun ya janyo cecekuce acikin sojoji da masana shari’a musamman ganin yadda mambobin rundunar da dama suke cikin mawuyacin hali a ayyukansu.
Saidai, yayin da yake ganawa da manema labarai a Abuja Daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Markus Kangye ya ce za su cigaba da bin dokokin HTACOS har zuwa lokacin da za a shigar da hukuncin cikin dokar ƙasa a hukumance.
