Hundeyin ya zama sabon kakakin ƴan sanda

Spread the love

Sifeton rundunar ƴan sandan, Kayode egbetokun ya naɗa CSP Benjamin Hundeyin a matsayin sabon mai magana da yawun rundunar ƴan sanda a mataki na ƙasa (FPRO)

Naɗin Hundeyin na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar mai barin gado, Muyiwa Adejobi ya fitar.

‎”Babban Sifeton ƴan sandan ya buƙace shi da aiki da ƙwarewarsa ta sadarwa wajen inganta aikin ɗan sanda a Nijeriya ta hanyar ƙarfafa hulɗa da jama’a,” inji sanarwar.

Kafin sabon muƙamin, CSP Benjamin Hundeyin ya kasance kakain rundunar ƴan sanda reshen jihar Legas, inda ya kwashe shekaru yana aiki a matsayin.

By Babaji