Hidimar farauto labarai aikin sadaukar da kai ne, cewar Sarkin Dass

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Mai Martaba Sarkin Dass a Jihar Bauchi, Alhaji Usman Bilyaminu Othman, ya bayyana cewa, hidimar tattaro labarai, domin yaɗa su ga jama’a, a matsayin wata aikin sadaukarwa, don haka ya jinjina wa ‘yan jarida bisa ƙwazo, himma da juriyarsu wajen gudanar da ayyukansu na halasci.

Sarkin, dangane da haka, sai ya yi kira ga hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki su tabbatar da bai wa ‘yan jarida isasshiyar kariya yayin gudanar da ayyukansu na farauto labarai domin amfanin jama’a.

Ya ce, “Yayin da mutane ke gujewa wani lamari, ku kuma kuna tunkarar wajen, kuna kutsa kawunan ku cikin wurare masu hatsari, kuna nunuƙa kawunan ciki domin zaƙulo abubuwan da ke faruwa tare da bijiro muhimman bayanai da zasu amfani jama’a, ayyukan ku na sadaukar da kai ne, ina matuƙar jinjina maku bisa wannan ƙoƙari.”

Sarkin na garin Dass dai, yana jawabi ne ranar Talata data gabata, yayin da ya ke karɓar tawagar ‘yan jarida, ƙarƙashin ƙungiyar su ta ƙasa (wato NUJ) reshen Jihar Bauchi, waɗanda suka kai masa caffar ban girma a fadar sa dake garin Dass, kasancewar wani vangare na bikin shekara-shekara na qungiyar, wanda za a shafe kwanaki bakwai ana gudanar wa.

Othman ya bayyana cewar, “A wannan yanayi na rashin tsaro, da rashin faruwar al’amura, kun kasance jajirtattu da taurin zuciya kan ayyukan ku na yaɗa labarai, wannan abun ƙarfafa zuciya ne. ina da tabbacin za ku iya yin fiye da haka bisa samun kyakkyawan yanayi.”

Alhaji Usman Bilyaminu Othman, don haka ya jaddada bukatar a samar wa manema labarai tukwici ko tsari na wadataccen albashi daga hukumomi da kamfanoni dake ɗaukar su yin ayyukan farauto labarai ta yadda zasu gudanar da ayyukan su bisa adalci da rashin zargi.

Ya kuma gargaɗi ‘yan jarida da su doge wajen fayyace gaskiya komai ɗacin ta, yana nusar da su buqatar masu nuna adalci, ladabi, ƙarfin zuciya, da nuna gwanance wa bisa aiyukan su, la’akari da cewar, al’umma ta dogara ne kwacakwam akan su bisa samun tabbatattun labarai.

Da ya ke yin jawabi tunda farko, shugaban ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa, reshen jihar Bauchi, Kwamred Umar Sa’idu ya bayyana cewar, bikin na wannan shekara zai mayar da hankali ne kan fayyace ayyukan yau da kullum na mambobi da zummar cewa ana tafiya kan sahihiyar hanya da za ta kai damo ga harawa.

Ya bayyana cewar, cikin bukukuwan na tsawon maku guda, za a karrama mambobi da suka yi fice kan gudanar da ayyukansu na yau da kullum domin baiwa ɗaukacin mambobin ƙungiyar ƙwarin gwiwar aikata abubuwan da suka kamata dangane da ayyukan watsa labarai.

Kwamred Umar Sa’idu sai ya yabawa Sarkin Dass bisa samun tubarrakai daga gare shi a matsayin sa na Uba, yana mai bayyana cewar, ƙungiyar ‘yan jarida tana matukar jin daɗin nasihohi da shawarwari da take samu daga gare shi, waɗanda ya ce, suna taimaka wa wajen gudanar da ayyukan su na farauto labarai.