Daga SULAIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
A wani mataki na bunƙasa harkokin noma da samar wa matasa aikin yi domin su dogara da kansu tare da ƙara wadatar abinci a ƙasar nan, Hukumar Raya Kogunan Hadeja-Jama’are (HJRBDA) ta horar da matasa maza da mata 2,000 kan dabarun noma na zamani.
Shirin horon ya haɗa da raba matasan gida huɗu, inda aka horar da matasan 500 kan noman ban-ruwa ta ƙasa, yayin da wasu 500 aka koya musu yadda ake noma ta hanyar Green House. Haka kuma, an horas da wasu 500 kan dabarun noman gida ta amfani da buhu ko kwali, yayin da ragowar 500 aka koya musu yadda ake noman abincin dabbobi.
Da yake jawabi bayan ƙaddamar da cibiyar horar da matasa kan noman zamani, Ministan Albarkatun Ruwa da Tsafta, Injiniya Joseph T. Utsev, ya bayyana shirin a matsayin wata muhimmiyar dama ta tallafawa ƙasa wajen bunƙasa noma da tattalin arziki. Ya ce shirin ya yi daidai da manufofin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na samar da wadataccen abinci da kuma rage zaman banza tsakanin matasa.
Ministan ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da irin waɗannan shirye-shirye har sai Nijeriya ta rage ko ta daina dogaro da shigo da abinci daga ƙasashen waje. Ya kuma taya matasan da aka horar murna tare da kira gare su da su yi amfani da ilimin da suka samu domin ci gaban kansu da ƙasa baki ɗaya.
A nasa jawabin, Manajan Daraktan HJRBDA, Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi, ya bayyana cewa shirin yana daga cikin kudurorin gwamnatin tarayya na bunƙasa noma domin samar da wadataccen abinci. Ya ce manufar shirin ita ce bai wa matasa damar yin noma sau uku ko huɗu a shekara maimakon sau ɗaya da ake yi a baya.
A wani ci gaba, Ministan ya kuma ƙaddamar da aikin gina magudanar ruwa a ƙaramar Hukumar Jahun ta Jihar Jigawa, inda ya ce aikin zai taimaka wajen magance matsalar ambaliyar ruwa da ta daɗe tana addabar yankin.
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi Dan-Modi, wanda Mataimakinsa Injiniya Aminu Usman Gumel ya wakilta, ya yabawa gwamnatin tarayya bisa kawo wannan aiki, tare da yin kira ga al’ummar yankin da su bai wa masu aikin cikakken goyon baya.
Haka kuma, Ministan ya ƙaddamar da aikin gina madatsar ruwa da gonar gwaji a ƙaramar Hukumar Bichi, inda ya ce aikin zai ci kusan Naira biliyan 1.5, kuma ana sa ran kammala shi cikin shekaru uku. Ya bukaci ɗan kwangilar aikin da ya tabbatar da inganci da kammala shi cikin lokaci.
