Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin jihar Sakkwato ta ƙaddamar da sayar da takin zamani ga manoman jihar a farashi mai rahusa, wanda a cewar gwamnatin zai ba su damar gudanar da noman rani cikin sauƙi.
Gwamnan jihar, Ahmed Aliyu ne ya ƙaddamar da rabon takin a ƙaramar hukumar Wurno ta jihar a ranar Laraba 4 ga watan Fabrairu, inda ya ce inganta harkokin noma na cikin manyan ƙudurorin gwamnatinsa.
Gwamnan ya ce sun sayo tirela 52 na takin Urea da tirela 50 na NPK, kuma za a raba su ne ga ƙananan hukumomin jihar guda 23.
“Kowace ƙaramar hukuma za ta samu tirela biyu na Urea da tirela ɗaya na NPK, kuma za a sayar ne a farashi mai rahusa.”
Ya ce gwamnati ta rage kashi 62 a farashin takin NPK, da kashi 60 a tankin Urea, sannan ya ce sun yi haka domin ƙananan manoma su samu taki. “Sau uku muna raba takin kyauta a baya, amma sai muka lura asalin manoman ba sa samu. Shi ya sa muka ɓullo da wannan tsarin na sayar da takin kai-tsaye a farashi mai rahusa, sannan muka yi tsarin aiwatar da rabon a bayyane domin ya isa inda ake so.”
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta bayar da kwangilar gyara madatsar ruwa ta Lugu, sannan ya ce nan gaba za a gyara ta Kware domin amfanin masu noman rani, sannan ya ƙara cewa za su sayo tarakta guda 250 domin sauƙaƙa wa manoman aiki.
