Kaduna: Mutane 82 da ‘yan bindiga suka sace sun shaƙi iskar ‘yanci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kiristoci guda 82 da aka yi awon-gaba da su a lokacin da suke ibada a cocin Ƙauyen Kurmin Walin Ƙaramar Hukumar Kajurun Jihar Kaduna sun shaƙi iskar ‘yanci a ranar Alhamis.

An samu nasarar haka ne bisa wani shiryayyen atisaye da ya ƙunshi gwamnatin jihar da Ofishin Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (ONSA) da kuma Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS), kamar yadda Gwamna Uba Sani ya tabbatar.

Uba Sani ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara ga waɗanda al’amarin ya shafa a cibiyar kula da mata da yara a Kaduna inda ake ba su kulawar lafiyar jiki da ƙwaƙwalwa.

A ranar 18 ga watan Junairu ne aka yi garkuwa da mutane da dama ciki har da su, inda wasu rahotannin farko suka ce aƙalla waɗanda aka sacen sun kai guda 177.

Akan haka ne Gwamna Sani ya bayyana kaɗuwarsa ga mutanen da iyalansu, inda ya bayyana harin a matsayin abin da ya jefa jama’a cikin ƙunci, sannan ya tabbatar wa ‘yan ƙauyen cewa ana cigaba da ƙoƙarin ceto sauran waɗanda ke hannun ‘yan bindigar.

Ya kuma yaba wa tsarin tsaron gwamnatin Kaduna, ONSA, DSS da sauran hukumomin tsaro bisa abin da ya kira da ƙwarewar aiki wajen amfani da basira.

A ƙarshe, ya yi kira ga mazauna da su cigaba da taimaka wa hukumomin tsaro da bayanai akan lokaci domin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.

By Babaji