Hukumar ‘Civil Defence’ ta haramta ayukkan jami’anta na sa-kai a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Hukumar samar da tsaro ga farin kaya ta Civil Defence ta haramta ayukkan jami’anta na sakai a Sakkwato wato boluntiya da ke aiki ƙarƙashin hukumar.

Ɗaukar wannan matakin da hukumar ta yi dai ya biyo bayan yawaitar zarge-zargen aikata ababen da suka saɓa wa doka daga jami’an hukumar na sa kai.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar wadda ke ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar da ke Jihar Sakkwato, Hamza Adamu Illela, hukumar ta bayyana cewa izuwa yanzu ta dakatar da dukkan ayyukkan waɗannan jami’an sa kai saboda samun su da laifuka a yayin aikin gamayyar tsarkake wasu wurare a Ƙaramar Hukumar Sakkwato ta Kudu.

Bisa wannan ne hukumar ta sanar da dukkan jama’a kan cewa, su kai rahoton duk wani jam’in sa kai da suka gani yana aikata wani aiki da sunan hukumar a faɗin jihar Sakkwato.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *