Hukumar HISBAH ta kama wasu matasa biyu da zargin aikata baɗala a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Hukumar Hisbah reshen ƙaramar hukumar Dutsin-ma, ƙarƙashin jagorancin Kwamanda Shafi’u Ibrahim, ta samu nasarar kama wani saurayi tare da wata budurwa a wani gida da ke bayan Motel Dutsin-ma, inda ake zargin suna aikata baɗala.

Wannan nasara ta samu ne bayan da hukumar ta karɓi ƙorafe-ƙorafe daga wasu mazauna yankin masu kishin tarbiyya da zaman lafiya, waɗanda suka bayyana damuwarsu kan yadda ake gudanar da wasu ayyuka da suka saɓa wa ɗabi’a a cikin gidan.

Bayan samun bayanan sirri da kuma gudanar da bincike, hukumar ta tura jami’anta domin tabbatar da sahihancin rahoton. Samamen wanda OC G&C Haruna M. ya jagoranta tare da wasu jami’an hukumar ya kai ga cafke waɗanda ake zargin a wurin.

Binciken farko ya nuna cewa ana amfani da wasu gidajen da ɗalibai ke haya wajen aikata ayyukan da suka saɓa wa tarbiyya da koyarwar addini, musamman a lokutan hutun makaranta da ɗakunan kan kasance babu mazauna na asali.

Hukumar hisbah ta bayyana damuwarta kan yadda wasu matasa ke amfani da irin waɗannan wurare wajen gudanar da ayyukan da ke iya lalata tarbiyyar al’umma, tare da jawo matsaloli ga zaman lafiya da tsaron unguwanni.

Hukumar ta ya kira ga iyaye, masu gidaje, shugabannin al’umma da mazauna yankunan da ke kusa da ɗakunan kwanan ɗalibai da su kasance masu sa ido tare da gaggauta sanar da hukumar duk wani abu da ya yi kama da aikata laifi ko rashin ɗa’a.

Hukumar ta jaddada aniyarta na ci gaba da yaƙi da duk wani nau’in miyagun ɗabi’u da ke barazana ga tarbiyya da kyawawan halaye a cikin al’umma, tare da tabbatar da bin doka da oda a faɗin ƙaramar hukumar Dutsin-ma.

By ukarofi

Leave a Reply