Daga USMAN KAROFI
Hukumar SEC ta fitar da gargaɗi ga ‘yan Najeriya da su guji zuba jari a cikin kudaden intanet na Zugacoin da Samzuga GPT. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, hukumar ta bayyana cewa waɗannan kuɗaɗen ba su da izini kuma ba a yi wa masu rijista da hukumar ba domin gudanar da wata harkar kasuwa a Najeriya.
SEC ta ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa Zugacoin da Samzuga GPT nau’in Meme coin ne, wato kuɗaɗe da ba su da wata fa’ida ko amfani kai tsaye a zahiri, sai dai suna dogaro da hayaniyar masu tallata su ko ƙungiyoyin da ke bayansu. Hukumar ta yi gargaɗi cewa irin waɗannan kuɗaɗen su kan faɗa cikin dabarar damfara ta “pump and dump” inda ake tayar da darajarsu da yaudara sannan a siyar da su a lokacin da suka yi tsada, kafin su faɗi ƙasa su bar masu zuba jari cikin hasara.
A ƙarshe, hukumar ta shawarci jama’a da su daina siye ko tallata irin waɗannan kuɗaɗen intanet na ƙarya. Ta kuma buƙaci mutane su tabbatar da sahihancin kowanne irin kuɗin dijital ko masu tallata su ta hanyar duba jerin masu rijista a shafin yanar gizon hukumar: www.sec.gov.ng/cmos kafin su zuba jari.
