
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Namadi Sambo, ya yi watsi da rahoton da ke cewa ya koma jam’iyya mai mulki ta APC.
A sanarwar da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Umar Sani ya fitar, Namadi ya bayyana hakan a matsayin abinda aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al’umma.
Sanarwar ta kuma ce, hoton da ake yaɗawa a jikin labarin, wanda aka gan shi tare da Gwamna Uba Sani na Kaduna kuma da ke ƙoƙarin gaskata labarin, an yi shi ne tun da jimawa.
Haka kuma, sanarwar ta jaddada cewa, tsohon mataimakin shugaban ƙasar yana nan daram a PDP a matsayinsa na ɗaya daga cikin masu yi wa yi wa jam’iyyar biyayya, wanda kuma ba shi da ra’ayin sauya sheƙa a yanzu.
