Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban kwamitin harkokin cikin gida na Majilisar wakilai Hon Abdullahi Aliyu Ahmad ya gina rijiyoyin burtsatse guda 71 a mazaɓar sa ƙananan hukumomin Musawa da Matazu a Jihar Katsina.
A mazaɓu 10 da ke ƙaramar hukumar Musawa an gina guda uku,sai kuma cikin garin Musawa aka gina guda huɗu kasancewar hedkwatar ƙaramar hukumar.
Ita ma ƙaramar hukumar Matazu a gina rijiyoyin guda huɗu a garin Matazu, hedkwatar ƙaramar hukumar,sai sauran mazaɓun aka gina guda uku kowanne.
Mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai na ɗan majalisar Francis Sardauna ya faɗawa manema labarai a wata takardar sanarwa da ya fitar.
Ya ce kowace rijiyar an katange domin kare ta daga ɓatagari.
Kuma za a kafa kwamiti na mutanen yankin da za su kula da kowacce rijiya da kuma ƙayyade yadda mutane zasu rinƙa amfani da rijiyar.
Dujiman ya bayyana cewa samar da wannan rijiyoyin burtsatse a mazaɓar sa zasu magance cututtuka irin su amai da gudawa da sauran su.
Sardauna ya bayyana cewa ɗan majalisar ya taya al’ummar yankin murnar samun wadataccen ruwan sha da kawo ƙarshen wahalar da suka daɗe suna fama da shi na rashin ruwan.
Dujiman kuma yayi wa al’ummar mazaɓun sa na cigaba da kawo masu abubuwa na cigaban yankin.
Zan haɗa kai da gwamnatin tarayya da na Jihar Katsina wanda samar da dawamammen zaman lafiya a yankin da jihar baki ɗaya”,inji Dujiman Katsina.
Samarwa matasa aikin yi, ilimi,kiwon lafiya da taimakawa harkar noma kamar yadda na taimaka a baya”,Ɗan Majalisar ya ce
