
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ƴan sanda a Abuja, ta ƙaddamar da bincike akan wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen watsa labarai, wanda ke nuna yadda aka wata mata an ɗaure mata hannaye ta baya a wani ɗakin otal a yankin Gwarimpa dake birnin tarayya.
Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta bayyana hakan a wata takarda, ranar Laraba, inda ta ce hukumar ta samu labarin yaɗuwar bidiyon wanda ake cecekuce akansa.
Ta ce, tuni aka baza jami’ai zuwa wajen da ake zargin faruwar al’amarin a ƙarƙashin kwamishinan ƴan sandan Abuja, Ajao S. Adewale, wanda ya umarci a gudanar da bincike mai zurfi akan al’amarin.
Wani bincike a matakin farko ya nuna cewa Aladi Ofiskwu Johnson shi ne sunan matar, wadda asalinta ƴar Jihar Benuwai ce.
An ruwaito cewa, ta ziyarci otal ɗin ne wanda ke ‘3rd Avenue’, Gwarimpa a ranar 16 ga watan Yuni, 2025 tare da wani mutum wanda daga bisani ya fice daga otal ɗin va tare da ita ba.
Daga bisani, wani ma’aikacin gidan ya je ɗakin da suke, inda ya samu matar cikin mawuyacin hali, lamarin da ya sa aka gaggauta sanar da ƴan sanda.
A yayin binciken likitanci ne aka gano cewa ta rasu.
Rundunar ta kuma shawarci ƴan mata da su riƙa kula wajen zaɓar waɗanda siek hulɗa da su musamman waɗanda ba a san su ko asalin su ba.
