‘Yan sanda a Katsina sun kama riƙaƙkun ɓarayi biyu da wata mata mai ɓoye kayan sata

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Dubu ta cika ta wasu gungun ɓarayin da suka fasa wasu gidaje a unguwar ƙwaɗo, kambarwa da bayan ginin NYSC a garin Katsina.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya faɗawa manema labarai a ofishin shi.

Ya ce yanda suka kama waɗannan ɓarayi masu suna Lawal Hamza da aka fi sani da Honourable da ɗan shekara 28 da ke zaune a unguwar Saulawa da Nafi’u Sanusi ɗan shekara 33 da ke zaune a GRA, Katsina.

Waɗannan matasa sun sami nasarar fasa gidaje da dama a unguwanni ƙwaɗo da Kambarwa inda suka kwashe kayayyaki da suka haɗa da Talabishin ƙirar Plasma da Firijin, da tarin mabuɗai.

DSP Sadiq ya bayyana cewa binciken da ‘yan sanda su kayi ya sa suka gano ma mallaki kayan mai suna Muhammadu Lawal wanda ke zaune a unguwar Saulawa.

Haka ɓarayin sun ambaci wani abokin hulɗar su mai suna Abdulrahaman Sama’ila da ‘yan sanda ke nema ruwa a jallo.

Haka kuma ‘yan sanda sun kama wata mata mai suna Binta Ibrahim da ke zaune Sabuwar Unguwa da kayan sata da suka haɗa da kayan zannuwa na mata da na’urar samar da wuta mai amfani da hasken rana da sauran su.

Binta ta tabbatar da kayan sata ne,kuma ta same su ta hannun Lawal Hamza da ake zargi da zama jagoran ɓarayin.

DSP Abubakar Sadiq ya ce ‘yan sanda na nan na cigaba da bincike domin gano sauran kayan da kuma gurfanar da masu laifin a gaban kotu.

By ukarofi