Daga AISHA ASAS
Masu karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na jarida mai farin jini, Blueprint Manhaja. Kamar yadda muka kwashe sati har biyu muna tattaunawa kan abinda ya shafi bilicin, tun daga ma’anar sa da yadda ake yin sa zuwa shawara ga waɗanda ke son fara yin bilicin, tare da illolin da ke ciki.
A wannan makon da yardar mai dukka, za mu kai ƙarshen darasin.
7. Idan ka fara kana son ka daina, wacce hanya za ka bi?
Daina amfani da kayan bilicin na buƙatar haƙuri da shiri, domin akwai wasu illolin da ke iya fitowa yayin da sinadarai ke barin jiki. Ga wasu matakai:
Ziyarci likitan fata, domin tantance irin gyaran da fata ke buƙata.
Amfani da sunscreens da sabulai masu laushi da ba su da sinadarai masu guba.
Launin ki, darajar ki:
A ƙarshe ina son in ja hankalin mata kan cewa, launin fata bai kamata ya zama babban lamari da ake hango kyau idan akwai shi. Kyawun fata yana daga lafiyarta, tsaftarta, da kuma yadda mutum ya amshi kansa kamar yadda Allah Ya halicce shi.
