Mele Kyari ya shiga tsaka-mai-wuya bayan Majalisar Dattawa ta bai wa NNPCL mako guda ya bada ba’asin tiriliyan N210 da suka ɓata

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Dattawa ta bada wa’adin mako guda ga Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa ya gabatar da bayani dalla-dalla game da ɓatar wasu maƙudan kuɗaɗe da adadinsu ya kai kimanin sama da tiriliyan N210 daga rahoton bayanan kuɗaɗe tun daga shekarar 2017 zuwa 2023.

Kwamitin Majalisar akan kuɗaɗen al’umma, wanda ya yi nazari akan rahotannin kamfanin ya bada umarnin, bayan nuna damuwa akan wasu kuɗaɗe da aka kashe da waɗanda suka shigo ba tare da yin gamsassun bayanai akansu ba.

Ana ganin hakan zai jefa Mele Kyari cikin matsala duba da cewa shi ne tsohon shugaban kamfanin a wancan lokacin. A shekarar 2019 aka naɗa shi inda kuma ya sauka a 2025.

A yayin zaman Majalisar na ranar Laraba, an samu halartar Dapo Segun, wanda shi ne shugaban ɓangaren kula da kuɗaɗe da wasu manyan jami’an kamfanin, inda a jawabin da aka samu cikin rahoton NNPCL da suka gabatar, an samu bayanai da dama da suke cin karo da juna.

Shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wadada ya bayyana hakan a matsayin abinda aka yi domin cimma wata manufa wadda ba za su amince ba, yana mai cewa lallai sai an tabbatar da adalci a kai duba da halin matakin kuɗin shiga na gwamnati.

Ya ce, idan aka haɗa jimillar kuɗaɗen da aka ware domin kashe su a wasu ayyuka da na wasu kwangiloli da ba a gabatar da bayanai gamsassu akansu ba, sun kai Naira tiriliyan 210.

Sannan, ya bayyana cewa kwamitin ya miƙa tambayoyi guda 11 ga NNPCL tare da jiran amsoshinsu nan da sati ɗaya.

By Babaji