Hukumar tace fina-finai ta Kano ta bayyana waɗanda su ka yi nasara a gasar rubutu

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Abba El-Mustapha, ta fitar da sunayen mutum 50 da suka samu nasara a zagayen farko na gasar rubutun Hausa. Gasar ta samu halartar marubuta 126 daga sassa daban-daban, inda aka gudanar da tantancewa domin zaɓar waɗanda suka cancanta.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana cewa sunayen da aka fitar ba su nuna matsayin wanda suka yi nasara daga na farko zuwa na ƙarshe ba tukuna. “Za a ci gaba da tantancewa har zagayen ƙarshe, inda za a bayyana waɗanda suka samu gurbi daga na ɗaya zuwa na uku, sai kuma daga na huɗu zuwa na goma 15, sannan daga na 16 zuwa na 50,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa dukkan waɗanda sunayensu suka fito za su samu kyaututtuka gwargwadon matsayinsu a gasar. Hukumar ta bayyana cewa na farko zai samu Naira 500,000, na biyu Naira 300,000, yayin da na uku zai samu Naira 200,000.

Na huɗu zuwa na 15 za su samu kyautar Naira 30,000 kowannensu, sai kuma daga na 16 zuwa na 50 za a ba su kuɗin alƙalami har Naira 15,000.

Hukumar ta yi kira ga waɗanda ba su samu nasara a wannan zagaye ba da su ƙara jajircewa tare da sake shiga gasar a nan gaba.

Hukumar ta kuma yi godiya ga dukkan marubutan da suka shiga gasar da kuma goyon bayan da ake bai wa harkokin rubutu da adabi a Jihar Kano.

By ukarofi