Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

A ranar Lahadi, matatar man Ɗangote ta sanar da rage farashin man fetur (PMS) zuwa Naira 970 kan kowace lita ga ‘yan kasuwa. Babban jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin, Anthony Chiejina ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta ce matakin ya zama wata hanya ta godewa ‘yan Nijeriya saboda goyon bayansu wajen ganin matatar ta tabbata. Wannan saukar farashi ya biyo bayan tsohon farashin Naira 990 da aka sanar tun farko a cikin watan nan.

Hakazalika, sanarwar ta yaba wa gwamnati kan goyon bayanta, tana mai cewa wannan rage farashi zai taimaka wajen ƙarfafa kasuwancin cikin gida da bunƙasa jin daɗin al’umma. An kuma jaddada cewa matatar ba za ta sassauta ingancin kayanta ba, tare da tabbatar da samar da kayayyaki masu inganci.

Matakin rage farashin zai bai wa ‘yan kasuwa damar samun rarar Naira 20 kan kowace lita ta man fetur da aka saya daga matatar dake Lekki, lamarin da ake fatan zai ƙara ƙarfafa samar da man a cikin gida don kawar da fargabar ƙarancin mai.

By ukarofi