Na kusa na zama mashayi a baya – Obasanjo

Spread the love

Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi kira ga matasan Nijeriya da ɗalibai su guji amfani da miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa ba su da wata fa’ida ga rayuwa sai dai lalata ta kawai. Ya bayyana hakan ne a garin Abeokuta, jihar Ogun, a yayin taron ƙarawa juna sani kan yaƙi da shaye-shaye karo na biyu, wanda ƙungiyar Recovery Advocacy Network ta shirya mai taken “Fly Above The High”.

Obasanjo, wanda ya nuna damuwa kan yadda matsalar shaye-shaye ke ƙara yawaita a Nijeriya da yankin Yammacin Afirka, ya roƙi matasa su ɗauki matakin gujewa shaye-shaye. Ya kuma yi bayani kan wa’adin shugabancinsa na kwamishinonin Yammacin Afirka kan yaƙi da shaye-shaye ƙarƙashin asusun Kofi Annan Foundation, inda ya ce ya koyi cewa Yammacin Afirka ba kawai cibiyar safarar miyagun ƙwayoyi ba ce, har ma wurin shan ƙwayoyi.

Obasanjo ya bayyana yadda suka zagaya yankin Yammacin Afirka suna tsammanin cewa wurin ya tsira daga cutar shaye-shaye, amma sai suka gano cewa yankin ya zama cibiyar amfani da miyagun ƙwayoyi. Ya ce, “Shekaru sama da goma kenan da muka gano haka, kuma matsalar ta yi muni fiye da yadda take a wancan lokacin. Wannan yanayin da ke Yammacin Afirka yana shafar sauran sassan Afirka baki ɗaya.”

Haka zalika, tsohon shugaban ya tuna yadda ya fara shan sigari a lokacin matashinsa, amma tari mai tsanani ya sa shi ya daina. Ya yi gargadin cewa duk wanda ya fara irin waɗannan abubuwa yana fuskantar haɗarin kamuwa da ɗabi’ar. Obasanjo ya bayyana cewa, “Babu abin da miyagun ƙwayoyi za su yi maka sai hallaka.” Ya kuma ƙarfafa masu fama da matsalar shaye-shaye su nemi taimako tare da yin kira ga al’umma da su guji ƙyamar waɗanda suka faɗa cikin wannan matsala.

By ukarofi