Gwamnatin Kaduna ta musanta zargin sayar da kadarorin gwamnati ga Mawaƙi Rarara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Jihar Kaduna ta musanta batun da ke yawo a kafafen sada zumunta na cewa ta sayar da wata kadara ta gwamnati ga Mawaƙi Dauda Rarara.

Ta ce, takardar da aka gabatar a matsayin shaida, tsagwaron ƙarya ce ta ƙunsa da kuma ƙoƙarin ruɗar al’umma don karkatar da hankulansu daga kyawawan ayyukan da Gwamna Uba Sani ke yi a Kaduna.

Mai magana da yawun gwamnatin jihar, Dakta Victor Bobai ya bayyana hakan a matsayin wani salo daga ƴan adawa na daƙile ƙoƙarin ciyar da jihar gaba da gwamnan ke yi da tabbatar da kawar da duk wani nau’i na rashawa.

Ya ce hakan ba zai sanyaya gwiwar gwamnan ba na, don haka ne ya tabbatar da cewa babu wata kadara ta gwamnati da aka sayer wa Dauda Rarara ko makamancin irin cinikin a ƙarƙashin gwamnatin.

Ya kuma ce waɗanda suka ƙirƙiri batun, ba za su yi nasara ba wajen ɓata wa gwamnan suna.

Har’ilayau, ya ce Gwamnatin Sanata Uba Sani za ta cigaba da aiki tuƙuru wajen taimaka wa masu rauni cikin talakawa da nakasassu da mata da matasa da kuma mutane masu buƙatu na musamman a jihar.

Daga ƙarshe, ya yi kira ga al’ummar jihar su kasance masu lura da watsi da duk wani batu na ƙarya da za a ruɗe su da shi.

By Babaji