
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dawo Nijeriya daga taron ƙasashen G20 da aka yi a ƙasar Brazil, a jiya Asabar.
A yayin taron ne Shugaban ƙasar ya goyi bayan ƙaddamar da taron dangi a tsakanin ƙasashen duniya wajen yaƙar yunwa da talauci acikin al’umma.
Ya kuma tattauna da Darakta-Manaja na Asusun Kuɗi na Ƙasa-da-ƙasa (IMF), Kristalina Georgieva wanda ya yaba wa Tinubu bisa kwaskwarima da ya ke wa ɓangarori daban-daban a Nijeriya.
Ya kuma yi kira ga IMF ɗin da ta tallafa wa ƙoƙarinsa na inganta harkokin tattali da wasu muhimman gyare-gyare da gwamnatinsa ke yi a ƙasar don samar da gobe mai kyau ga al’umma.
Cikin ƴan rakiyarsa taron akwai; Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar; Ministan Ci-gaban Kiwo da kuma Ministar Al’adu.
