
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta musanta batun korar ma’aikatan da suka mallaki shaidar karatunsu a makarantun da ba’a tabbatar da sahihancinsu ba daga ƙasashen Benin da Togo.
Hakan na zuwa ne bayan da tsohon Sanata daga Jihar Kaduna, Shehu Sani ya koka game da zargin korar wasu ma’aikatan gwamanti ta kafar X inda ya ce lamarin ya shafi dubunnan waɗanda suka kammala karatu a Jamhuriyar Benin.
Ya kuma roƙi gwamnati ta sake nazari game da lamarin tare da samar musu da mafita.
Saidai, Hukumar kula da Ma’aikata ta Ƙasa ta musanta batun korar da dama daga cikin ire-iren ma’aikatan.
Shugaban hukumar ta ofishin kakakinta, Taiwo Hassan, ya musanta batun a inda ya ce ba su samu wani karɓaɓɓen umarnin yin hakan daga gwamnati ba.
Ya jaddada matsayin hukumar na ɗaukar aiki, sauya waje, kora da hukuntawa wanda a halin yanzu ya ce ba su kai ga korar kowa ba.
A farkon shekarar nan ne Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya naɗa wani kwamiti da zai yi bincike game da zargin wasu kwalayen digiri da ba a yarda da su ba da aka ce ƙasashen maƙotan Nijeriya ke bada su.
Ya ƙara da cewa, akwai saƙon umarni daga ofishin Shugabar Ma’aikatar ma’aikata da zai bada dama ga gwamnati ta ware ma’aikatan da ake bincike akan su.
