Hukumar tace fina-finai ta Kano ta dakatar da Jaruma Samha

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta Jihar Kano ta dakatar da Sahma M Inuwa daga shiga harkar film na tsawon shekara ɗaya, tare da ƙwace shedarta ta zama halartacciyar ƴar fim.

Ta cikin wata sanarwar da jami’in yaɗa labaran hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya aikawa manema labarai ya shaida cewa hukumar ta sha alwashin ba za ta sake tace duk wani fim da Samha ta fito a ciki ba.

Wannan ya biyo bayan wasu ƙorafe-ƙorafe da al’umma su ka yi kan wani bidiyo da jarumar ta saki da ke nuna shigar da bata dace da koyarwar addinin musulunci ba, baya ga samunta da yin kalaman da basu dace ba.

Ya zuwa yanzu dai hukumar ta dakatar da Samha har tsawon shekara ɗaya a wani mataki na tabbatar da bin dokoki tare da ƙara tsaftace masana’antar Kannywood.

By ukarofi