WAEC ta ƙaddamar da shirin jarrabawa ta musamman ga ɗalibai a Janairu da Fabrairu

Spread the love

Hukumar shirya jarabawar Afirka ta Yamma (WAEC) ta sanar da sabon shiri da za ta fara a shekarar 2025, wanda zai bai wa ɗalibai damar sake rubuta jarabawar WASSCE a cikin watan Janairu da Fabrairu. Wannan sabon tsarin, wanda ake kira da WASSCE PC1, ya bambanta da tsohon tsarin da ya buƙaci ɗalibai su jira zuwa lokacin zagayowar jarabawar da aka saba duk shekara.

A wata hira da aka yi da shugaban hulɗa da jama’a na WAEC, John Kapi, a ranar Talata, 31 ga Disamba, ya bayyana cewa ɗalibai da suka duba sakamakonsu kuma suka ga buƙatar sake rubuta jarabawa za su iya yin rijista kafin 8 ga Janairu.

Ya ce jarabawar za ta gudana daga 24 ga Janairu zuwa 15 ga Fabrairu 2025. Haka kuma, hukumar za ta hanzarta sakin rahoton shugabannin masu duba jarabawa domin taimaka wa ɗalibai wajen fahimtar kurakurensu.

Hukumar ta sanar da cewa an yaɗa labarin wannan shiri ta kafafen yaɗa labarai, shafukanta na intanet, da kuma dandalin duba sakamako domin tabbatar da cewa ɗalibai da iyaye sun samu bayani game da wannan dama. Ɗalibai da aka soke sakamakonsu saboda wasu dalilai amma ba su samu hukunci na haramcin shekaru ba, za su iya yin rijista a wannan jarabawa.

Jarabawar dai za ta gudana ne a biranen jihohi saboda adadin ɗaliban da za su halarta bai da yawa.

WAEC ta yi kira ga ɗalibai su hanzarta yin rijista kafin 8 ga Janairu don su amfana da wannan dama, domin hakan zai taimaka musu su samu ƙarin maki cikin lokaci kuma su samu damar shiga matakin karatu na gaba ba tare da ɓata lokaci ba.

By ukarofi