
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Shugaban mulkin sojin Nijeriya, Ibrahim Babangida ya jaddada goyon bayansa ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu, yayin da tsohon Shugaban ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar ya yaba wa ayyukan Shugaban Nijeriyar da kira ga ‘yan ƙasa da su tabbatar da yin zaɓukan 2027 da ke tafe cikin lumana.
Tsofaffin shugabannin ƙasar sun faɗi matsayarsu ne a ranar Alhamis, a mabambanta ziyarce-ziyarce da tawagar shugaban ƙasa ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila ta kai musu a gidajensu na Minna da ke Jihar Neja. Tawagar, wadda kuma ta ƙunshi Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ta fara ganawa ne da Babangida a gidansa na Hilltop gabanin zuwa gidan Abdulsalami.
Da yake isar da saƙon Shugaba Tinubu ga manyan ƙasar, Gbajabiamila ya ce shugaban ya umarci da su kai musu ziyarar ban-girma da duba halin da suke ciki tare da kai masa rahoto. Ya ce, Tinubu ya kasance mai yawan ganawa da jagororin biyu, amma a yanzu ayyukan jagoranci da yaƙin neman zaɓe sun taƙaice masa aiwatar da wasu muhimman al’amura, yana mai ƙarawa da cewa sun ziyarci Gwamnan Jihar Neja kafin zuwa gidajen tsofaffin shugabannin ƙasar.
A ganawarsa da ‘yan jarida jim-kaɗan bayan ziyarce-ziyarcen nasu, Gbajabiamila ya ce Babangida ya bayyana gamsuwa ga ayyukan gwamnatin Tinubu, yana mai jaddada goyon bayansa ga shugaban tare da masa fatan alheri a zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar a Junairun 2027. Haka kuma, ya bayyana tsofaffin shugabannin ƙasar biyu a matsayin masu ruwa da tsaki masu muhimmanci waɗanda ba za taɓa manta gudunmawarsu ba ga tarihin siyasar Nijeriya.
Shi ma a nasa jawabin, Abdulsalami ya bayyana gamsuwarsa ga ayyukan gwamnatin Tinubu a lokacin da ‘yan jarida suka tambaye shi game da yadda yake kallon kamun ludayin shugaban Nijeriyar. Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su tabbatar da gudanar da zaɓukan da ke tafe a 2027 bisa zaman lafiya da lumana da ƙaurace wa dukkan abin da zai haifar da tayar da zaune-tsaye acikin al’umma.
Sauran ‘yan tawagar shugaban ƙasar sun haɗa da Mai Taimaka wa Shugaban Ƙasa akan Tsare-tsaren da Shirye-shirye, Hadiza Bala-Usman; tsohon Ƙaramin Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Yusuf Tanko Sununu; da tsohon Ministan Sufuri, Sa’idu Ahmed Alƙali, Mataimakin Gwamnan Jihar Neja, Yakubu Garba; mambobin Majalisar Wakilai, Abdulmumini Jibrin Kofa da Fuad Kayode Laguda; Mai taimaka wa Shugaban kan Harkokin Majalisar Dokokin Ƙasa (Majalisar Wakilai), Dakta Wasiu Olanrewaju-Smart; da kuma Darakta-Janar kuma Shugaban Ofishin Tattaunawar Kasuwanci na Ƙasa, Sanusi Rikiji.
