Mataimakin shugaban jam’iyyar ADC na jihar Kebbi Alhaji Musa Muhammed Dagwaya ya bayyana cewa yanzu idan ku ka ga wani ɗan jam’iyyar PDP a jihar Kebbi ɗan kwangila ne.
Ya yi wannan bayanin ne a garin Felande yayin wata ziyarar sada zumunci da ayarin sa ya kai ranar Lahadin da ta gabata.
Alhaji musa Dagwaya ya ce su ne suka zo da PDP suka yi rainon ta har ta bunƙasa kuma sun rusa ta babu labarin ta yanzu a Kebbi.
Duk mai hankali ya san akwai yan kwangila da ke yi wa gwamnatin APC aiki suna yaudarar mutane da sunan yayan jam’iyyar PDP ne amma dai yanzu Alhamdu Lillahi mutane sun ankara da ana so ne a yaudare su.
Ya yi kira ga al’umma da kada su aminta da su duk irin magiyar da suka zo da ita mayaudara ne APC su ke yi wa aiki.
Ya kuma nemi al’umma da su fito ƙwan su kwarkwata ranar zaɓe su jefa ƙuri’a kuma su kare ƙuri’a su ba tare da wani tashin hankali ba.
