Gwamnatin Katsina za ta gyara ƙarin makarantun firamare 68 a faɗin jihar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya amince da gyaran wasu ƙarin makarantun firamare 68 da suka lalace a faɗin jihar.

Wannan amincewa ta zama kashi na uku na shirin gaggawa na gwamnatin jihar na gyaran makarantun firamare da suka lalace, kamar yadda wata sanarwar manema labarai da Hon. Lawal Rufa’i Safana, Mai Ba Gwamnan Shawara kan binciken ƙananan hukumomi kuma shugaban kwamitin da ke kula da shirin, ya fitar.

Kwamitin ya ce makarantun 68 da aka zaɓa sun ƙunshi makarantu biyu daga kowace ƙaramar hukuma 34 na jihar.

Wannan kashi na baya ya biyo bayan gyaran makarantun firamare 136 da aka gudanar a matakan farko na shirin.

Makarantun da aka zaɓa suna cikin mazaɓu daban-daban na tarayya, ciki har da Bakori Danja, Matazu Musawa, Faskari Ƙankara, Sabuwa, Malumfashi, Kafur sai Funtua, Dandume da Katsina.

Sauran yankunan da shirin ya shafa sun haɗa da Ɓatagarawa Charanchi Rimi da kuma Batsari Safana Ɗanmusa, Dutsinma Kurfi, Jibia Kaita, Daura Sandamu, Mai’Adua, Bindawa, Mani, Zango Ɓaure, Mashi Dutsi da Ingawa, Kankia, Kusada.

Daga cikin makarantun da aka lissafo akwai makarantar firamare ta Maikwari da Kaɗanyar Baushe a Bakori; Rafin Barwa da Kabir Usman a Danja; Musa Mata da Kaura a Jibia; da kuma Galadima Abu da ke Yanɗaki da Modibawar Kaita a Kaita.

Kwamitin ya ce an tsara wannan shiri ne domin inganta yanayin makarantun firamare da samar da ingantaccen muhalli na koyo ga ɗalibai a faɗin Jihar Katsina. Ana gudanar da shirin ne ƙarƙashin kwamitin gaggawa na gyaran makarantun Firamare 10 da suka fi lalacewa a kowace daga cikin ƙananan hukumomin jihar 34.

By ukarofi

Leave a Reply