Idan wani abu ya faru da El-Rufa’i gwamnati ce ke da alhaki – Atiku

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa kuma jigo a jam’iyyar haɗaka ta ADC, Atiku Abubakar, ya ce iyalan tsohon gwamnan Kaduna, Naisr El-Rufa’i da abokansa da masu hulɗa da shi sun damu matuƙa kan lafiya da walwalarsa yana mai cewa idan wani abu ya faru da shi, gwamnati ce ke da alhakin hakan.

Atiku ya bayyana hakan ne a shafinsa na ɗ.

Ya ce “dole ne gwamnati ta fito ta fayyace wace hukuma ce ke tsare da El-Rufai, ko EFCC ko ICPC ko DSS ko wata hukumar tsaro ta daban.”

A cewarsa, “ɓoye bayanai a irin wannan yanayi na tsare mutum yana ƙara haifar da shakku a zukatan jama’a, alhali ‘yan ƙasa na da haƙƙin sanin gaskiya.

Atiku ya jaddada cewa duk hukumar da ke da alhakin tsare shi tana da nauyin kundin tsarin mulki na tabbatar da tsaronsa da mutuncinsa da samun kulawar lafiya, da kuma damar ganawa da iyalansa da lauyoyinsa.

Ya ƙara da cewa “rahotannin da ke cewa ya samu haɓo wato zubar jini ta hanci tare da zargin hana iyalansa ganinsa abin damuwa ne ƙwarai kuma ba abin amincewa ba ne a tsarin dimokuraɗiyya.”

Ya ce idan hukumomi ba za su iya tabbatar da lafiyarsa da haƙƙoƙinsa ba, to hanyar da ta dace bisa doka da jinƙai ita ce a ba shi beli ba tare da ɓata lokaci ba.

A cewarsa, “idan wani abu ya same shi, alhakin hakan zai kasance a kan gwamnati ne.

By ukarofi