‘Yan kasuwar Larabar Mata sun jajenta wa ‘yan kasuwar Singa kan Iftila’in gobara

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Shugaban Kasuwar Larabar Mata, Alhaji Umar Alasan ya jajentawa ‘yan kasuwar Singa bisa gobara da ta same su ‘yan kasuwar ya bayyana gobarar da cewa masifa ce babba da ta shafi kowa, domin Kano cibiya ce ta kasuwanci a ƙasar nan suna fata Allah ya mayar musu da alkhairi.

Ya yi kira ga shugabanni a matakin jiha da ƙasa da na ƙananan hukumomi da masu hali su duba  su taimaka a ɗauki matakai kan dukkan abinda ke jawo faruwar gobara irin wannan a duba a gyara ayi kandagarki sannan kuma a tallafawa wanda suka gamu da asara a sanadin gobarar.

Ya ƙara da yin kira ga ‘yan kasuwa kasancewar ana cikin kusantowar watan azumi na Ramadan  a sauƙaƙa kayayyakin masarufi  don al’umma su saya a cikin rahusa da sauƙi i a sami walwala a samu a yi ibada cikin kwanciyar hankali da natsuwa.

Alhaji Umar Alasan ya yi kira ga yan kasuwa akan  wannan gobara ta zama  izina  akan yan kasuwa su kula kowa ya sauke haƙƙin Allah dake kansa a kuma sassauta a tausayawa al’umma sai ubangiji ya kare musu dukiyarsu daga iftila.

Shugaban na kasuwar laraban mata yace Allah ya sawa  kasuwar  albarka,  kudu da Arewa gabas da yamma  al’umma na shiga cikinta  sosai tana kuma cigaba da bunƙasa, kasuwa ce da suma tasowa suka yi suka sameta  tun lokacinda turawa suke  zuwa suna bada magani ga masu cutar kuturta kasuwar ta kafu.

Ya ce dalilin da yasa  kasuwar  ta ci sunan Larabar  mata shine  idan turawa sun zo suna bada magunguna sai  mata dattijai da yan mata  sukan kawo kayan gargajiya suna sayarwa tun daga nan  ta sami wannan sunan.

Alhaji  Umar Alasan ya ce a lokacinda suka karɓi shugabancin kasuwar sun zo sun tarar da matsaloli amma cikin ikon Allah sun shiga  sun fita sun inganta  tsaro a cikin kasuwar da fahimtar juna  kuma jami’an tsaro na  yan sanda dana sa kai da shugabancin  kasuwa na bada gudummuwa don a zauna lafiya.

By ukarofi