Tinubu ga gwamnoni: Na ƙuduri aniyar ceto Nijeriya kuma za mu kafa ’yan sandan jihohi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya ce ya ƙuduri aniyar “ceto” Nijeriya tare da cika alƙawuran da ya yi wa ’yan ƙasa.

Shugaban ya bayyana hakan ne a Abuja a yammacin ranar Litinin yayin da ya karɓi bakuncin gwamnonin jihohi domin buda baki na haɗin gwiwa tsakanin Musulmi masu azumin Ramadan da Kiristoci masu azumin Lent a Fadar Shugaban ƙasa.

“A wannan lokaci mai tsarki ga manyan addinai biyu a ƙasarmu, muna tuna cewa fiye da siyasa da manufofi, mu mutane ne masu lamiri,” in ji Tinubu a shafinsa na ɗ.

Ya yaba wa gwamnonin kan ƙoƙarin da suke yi da kuma ayyukan tallafi da suka gudanarwa a wannan wata mai tsarki.

Sai dai ya ƙalubalanci su da su ƙara ƙoƙari wajen kai wa matashin da ke jin an manta da shi, su tallafa wa matar da ke ɗaukar nauyin iyalinta, da kuma isa ga al’ummomin karkara.

“Ci gaba bai kamata ya bambanta addini ba. Tausayi bai kamata ya bambanta ƙabila ba. Dama bai kamata ya bambanta matsayi ba.

“Na ƙuduri aniyar ceto wannan ƙasa. Kuma muddin muka haɗa kai wajen isar da fata ga ’yan ƙasa, mafi alheri na tafe ga Nijeriya. Abin da na yi wa ’yan Nijeriya alƙawari ba za a fasa ba.”

Ya ce tsaro shi ne ginshiƙin bunƙasar tattalin arziƙi, yana mai cewa noma, kasuwanci da iyalai ba za su bunƙasa ba idan babu tsaro.

Tinubu ya sake jaddada shirin gwamnatinsa na kafa ’yansandan jihohi, yana mai bayyana cewa gyara ne na zahiri ba siyasa ba.

By ukarofi